Gwamnan APC Ya Fadi Dalilinsa Na Ajiye Malanta Ya Tsunduma Siyasa
- Bayan shekara 33 yana hidimtawa coci, Gwama Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya shiga.harkokin siyasa
- Gwamnan ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin ceto al'ummar mutanen jihar daga halin talauci
- Tun bayan yanke shawarar ƙyale harkokin coci domin neman mulki, Gwamna Alia ya sha tambayoyi kan wannan matakin da ya ɗauka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benuwai - Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, na jam'iyyar APC ya yi ƙarin haske kan dalilinsa na shiga siyasa.
Gwamnan wanda babban fasto ne ya ƙyale harkokin coci inda tsunduma cikin harkokin siyasa.
Hyacinth Alia ya dai zayyano dalilansa na shiga siyasa ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Alia ya shiga siyasa?
Gwamna Alia ya yi nuni da cewa ya shiga siyasa ne saboda yana son ya ceto talakawan jihar Benue.
Da aka tambaye shi dalilinsa na tsunduma cikin siyasa, sai ya kada baki ya ce:
"Mutane da dama sun yi wannan tambayar. Amma wacce ta ɗauki hankalina sosai ita ce lokacin da Gwamna Soludo na Anambra ya ce min meyasa na ƙyale coci na zaɓi wahalar da kai na wajen yin mulki.
"Na gaya masa cewa amsar mai sauƙi ce. Coci tana da manufa, wacce ita ce ceto mutane. Coci ba ta son mutane su tagayyara. Abin da yasa na shiga siyasa shi ne cimma wannan manufa. Na zo ne domin na ceto mutanen Benuwai."
Gwamnan ya bayyana cewa kafin ya shiga siyasa ya yi aiki sosai da talakawa waɗanda yake ganin ba a ba su kulawar da ta dace.
"Kafin na shiga siyasa, na ga abubuwa da dama marasa kyau. Na kwashe shekara 33 a matsayin fasto cikin jama'a.
"Na shiga lungu da saƙo tare da su, kuma mutanen da nake jin daɗin aiki tare da su sune talakawa, waɗanda ba su da galihu a cikin al'umma.
Batun Alia na son Ganduje ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya musanta batun cewa yana son Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin APC.
Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe ballantana makama, inda ya ce yana goyon shugabancin Ganduje.
Asali: Legit.ng