Gwamnan Kano Ya Magantu Kan Naɗa Ɗan Kwankwaso a Matsayin Kwamishina

Gwamnan Kano Ya Magantu Kan Naɗa Ɗan Kwankwaso a Matsayin Kwamishina

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa ya nada dan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin kwamishina
  • Gwamnan jihar Kano ya ce Mustapha dan Kwakwanso yana daga cikin hazikan matasa da suka yi gwagwarmaya har aka kafa gwamnati
  • Ya bayyana cewa nadin da aka yi wa Mustapha a matsayin mamba a majalisar mukarrabansa ba wai an yi da nufin sakawa mahaifinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce ya nada Mustapha dan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin kwamishina saboda ya cancanta.

Gwamnan Kano ya yi magana kan ba dan Kwankwaso mukami
Gwamna Yusuf ya ce dan Kwankwaso matashi ne da aka nada bisa cancanta. Hoto: @Kyusufabba/@imranvashyr
Asali: Twitter

Yusuf ya ce dan Kwakwanso yana daga cikin hazikan matasan da suka yi aiki tukuru domin samun nasarar wannan gwamnati a Kano.

Kara karanta wannan

A wurin buɗa baki da manyan Malamai, Gwamnan APC ya rage farashin shinkafa da kashi 50

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, kamar yadda PM News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Biyan bashi ne nadin Kwankwaso?

A cewar sanarwar mai taken: “Don kare nadin Mustapha Kwankwaso,” nadin Mustapha ba biyan bashi bane kamar yadda wasu suke fada.

Dawakin Tofa ya ce Gwamna Yusuf yana ba matasa dama wajen nuna kwarewar da suke da ita, domin haka matsayin Kwankwaso ba shi zai hana a ba Mustapha mukami ba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Abba ya mika sunan Mustapha Kwankwaso da wasu mutum uku ga majalisar jihar domin a tantance a matsayin sabbin mukarrabansa.

Kwankwaso da sauran mutane uku

Har zuwa lokacin nadin nasa, Mustapha Kwankwaso na aiki ne matsayin shugaban wata babbar makarantar kudi mallakin mahaifinsa da ke Gwarinpa, Abuja.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

Sauran wadanda aka nada sun hada da Adamu Aliyu, Usman Karaye da Abduljabbar Garko.

Adamu Aliyu, tsohon kwamishinan filaye da tsare-tsare da Abba ya dakatar a watan Satumbar da ta gabata saboda barazanar kisa ga alkalan kotu zaben jihar.

Abba zai kafa sabbin ma'aikatu

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa a ranar Talata ne Gwamna Abba Yusuf ya rubutawa majalisar Kano bukatar neman a kafa sabbin ma’aikatu hudu a jihar.

A cewar wasikar da kakakin majalisar, Jibrin Ismail Falgore ya karanta a zauren majalisar, samar da sabbin ma’aikatun zai inganta ci gaban jihar.

Sabbin ma'aikatun sun hada da ma'aikatar harkokin jin kai, wutar lantarki da sabunta makamashi, tsaro na cikin gida, da ma'aikatar manyan ma'adinai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.