Kaduna: Alkawarin da Uba Sani Ya Yi Ga Daliban Kuriga 137 Bayan Hada Su da Iyayensu

Kaduna: Alkawarin da Uba Sani Ya Yi Ga Daliban Kuriga 137 Bayan Hada Su da Iyayensu

  • An ɓarke da farin ciki marar misaltuwa bayan Gwamna Uba Sani ya sada daliban makarantar Kuriga da iyalansu
  • Daliban sun gana da iyayensu ne a wani ƙayataccen bikin da aka gudanar a kan hanyar Katuru da ke birnin Kaduna
  • Wannan na zuwa ne bayan ceto daliban makarantar Kuriga 137 da aka yi bayan shafe kwanaki a hannun 'yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya haɗa daliban makarantar Kuriga 137 da aka sace da iyalansu.

Bikin wanda ya ƙayatar da jama'a an gudanar da shi ne a kan hanyar Katuru da ke birnin Kaduna.

Kara karanta wannan

AYM Shafa: Attajiri ya ware makudan kudi ga iyalan wadanda suka rasu wajen karbar zakkah

Uba Sani ya yi alkawari ga daliban makarantar Kuriga 137 a Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya haɗa daliban makarantar Kuriga 137 ga iyalansu. Hoto: Uba Sani.
Asali: Facebook

Murna da iyayen daliban Kuriga suka nuna

Daliban da iyayensu sun nuna jin dadinsu da kuma godiya ga Gwamna kan kokarin da ya yi wurin tabbatar da kubutar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdulkadir Meyere ya masu alkawarin daukar nauyin karatunsu har zuwa Jami'a.

Meyere ya roki iyayen da su ci gaba da addu'o'i domin samun ingantaccen tsaro a fadin jihar Kaduna, cewar Channels TV.

Martanin jama'ar yankin Kuriga ga Uba Sani

Wakilin jama'ar Kuriga, Idris Abdullahi (Madakin Kuriga) ya godeqa gwamnan kan ba da dukkan gudunmawa wurin ceto daliban.

Ya yabawa Gwamnatin jihar kan tarurruka da suka yi ta yi da sarakunan gargajiya kan wannan iftila'i, cewar Thisday.

A karshe, ya gode masa kan irin tallafi da ya ba 'yan yankin da kuma rokan Ubangiji ya kare su da faruwar bala'i irin wannan a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya tura sunan ɗan Kwankwaso da mutum 3 Majalisa domin tantancewa

A bangarensa, Sarkin Kuriga ya godewa Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu da Nuhu Ribadu da sauran jami'an tsaro.

An ceto daliban Kuriga a Kaduna

Kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya sanar da ceto daliban makarantar Kuriga 137 da aka sace a jihar a kwanakin baya.

Gwamnan ya godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da goyon baya da ya ba shi har aka samu nasarar ceto daliban.

Wannan na zuwa ne bayan sace daliban da 'yan ta'adda suka yi a kauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.