Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Easter 2 Na Shekarar 2024, Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu ga ma'aikata domin bukukuwan Easter na shekarar nan ta 2024
- Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
- Ranar Juma'a, 29 ga watan Maris ta zama ranar hutun 'Good Friday', yayin da ranar Litinin, 1 ga watan Afirilu ta zama ranar hutun Easter
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 29 ga watan Maris da Litinin 1 ga Afrilun 2024 a matsayin ranakun hutu.
An ware ranakun ne domin hutun bukukuwan 'Good Friday' da Easter Monday' na mabiya addinin Kirista na shekarar 2024.
Sanarwar hutun Easter a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, cewar rahoton jaridar The Nation.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako.
Ya buƙaci Kiristoci da dukkan ƴan Najeriya gaba ɗaya da su yi koyi da sadaukarwa da ƙauna da Yesu Almasihu ya nuna, rahoton jaridar The Punch.
Easter: Kiran gwamnati ga ƴan Najeriya?
A cewar ministan, bikin Easter bayan muhimmancinsa a adddini, yana ƙara danƙon zumunci, ƙauna da yafiya waɗanda ke da matuƙar muhimmanci wajen zaman tare.
Ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da su yi koyi da waɗannan ɗabi'u waɗanda za su kawo ci gaba a Najeriya ta hanyar samar da haɗin kai da rage faɗace-faɗace a tsakanin ƴan Najeriya.
Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa sadaka da taimakon marasa galihu a cikinsu domin tsamo su daga cikin halin da suke ciki.
Hakan a cewarsa, ya yi daidai da manufar 'Renewed Hope' ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A yayin da yake taya Kiristoci na ciki da wajen Najeriya murnar zagayowar Easter, ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su haɗa hannu da gwamnatin Shugaba Tinubu, a ƙoƙarinta na samar da ci gaba ga kowa.
Tinubu ya halarci jana'izar sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmeɗ Tinubu ya halarci jana'izar sojojin da aka kashe a jihar Delta.
Halartar jana'izar da Shugaba Tinubu ya yi, ta sanya ya zama shugaban ƙasa na farko da ya halarci binne sojoji cikin shekara 10.
Asali: Legit.ng