Abuja: Farashin Dala Ya Yi Babbar Faɗuwa Lokaci Guda a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
- Ƴan kasuwar canji sun musanta rahoton da ke yawo cewa farashin Dala ya ƙara karyewa, ya koma N1,000 kan kowace $1
- Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto ya karaɗe shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N1000 a Otal ɗin Sharaton da ke Zone 4 a Abuja
- A baya-bayan nan ne babban banki CBN ya ce zai sayar da $10,000 ga kowace ɗan canji kan farashin N1251/$1
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƴan kasuwa masu hada-hadar canjin kuɗi (BDCs) sun musanta rahoton da ke yawo a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter cewa Dala ta dawo N1,000.
A cewar ƴan canji, rahoton wanda ya yi iƙirarin farashin Dalar Amurka ya ragu zuwa N1,000 kan kowace Dala ɗaya ba gaskiya bane.
Rahotanni sun karaɗe manhajar X cewa Dala ra rushe zuwa N1,000/$1 a kasuwar ƴan canji da ke birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A safiyar yau a Zone 4 Abuja, daura da Otal din Sheraton, ana siyar da dala a kan N1,000/$1. Abdulsalam BDC yana sayar da ita a farashin N900 ga duk wanda zai sayi sama da $5,000.
"Ana ta rige-rigen sayar da daloli a Zone 4. Dala a kasuwar hada-hadar kudi ta ƴan caji a halin yanzu ta faɗi warwas, ana siyar da ita a farashi mai rahusa fiye da farashin gwamnati," in ji rahoton.
Menene gaskiya kan saukar Dala?
Sai dai wakilin Punch ya tuntubi “Abdusallam BDC” watau Abubakar Abdusallam a ranar Talata a Abuja, kuma ya musanta cewa yana sayar da Dala a kan farashin N900-N1000.
“Muna sayar da Dala a kan farashin N1300/$1, ba N1000 ko N900 ba,” inji shi.
Wani mai amfani da manhajar X, wanda ba a iya tantance sunansa na gaskiya ba, shi ma ya karyata jita-jitar, inda ya bayyana cewa yana Otal ɗin Sheraton kuma ba haka farahin yake ba.
Bankin CBN ya saida Dala a N1200
Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa babban bankin Najeriya ya yi tayin sayar da Dala 10,000 ga kowane ɗan kasuwar canji kan kudi N1,251/$.
Babban bankin CBN yana sa ran kada ƴan canjin su sayar da Dala sama da N1,269/$, ma'ana ribar da za su ɗora ba za ta wuce N18 ba.
CBN ya biya bashin $7bn
A wani rahoton na daban kun ji cewa a kokarin farfaɗo da darajar naira a Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauki hanyar kawo karshen matsalar.
Bankin karkashin jagorancin Yemi Cardoso ya biya bashin $7bn da ya gada daga tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.
Asali: Legit.ng