Jerin sunayen kwamishinonin jihar Kano da ma'aikatunsu

Jerin sunayen kwamishinonin jihar Kano da ma'aikatunsu

A ranar Talata ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bawa sabbin kwamishinonin da ya rantsar ma'aikatu. An yi rantsuwar ne a filin wasa na Sani Abacha.

Mataimakin gwamnan jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne kwamishinan aikin gona. Muratala Sule Garo ne ya samu ma'aikatar kananan hukumomi ta jihar.

Injiniya Muazu Magaji ne kwamishinan aiyuka inda Barrister Ibrahim Mukhtar ya koma ma'aikatarsa ta shari'a a matsayin kwamishina.

An rantsar da Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin kwamishinan raya karkara inda Dr Kabiru Ibrahim Getso aka rantsar dashi a matsayin kwamishinan muhalli.

Hakazalika, Kwamared Mohammed Garba ya koma ma'aikatarsa ta yada labarai a matsayin kwamishina inda Mohammaed Dakadai ya bayyana a matsayin kwamishinan kasafin kudi da tsari na jihar.

DUBA WANNAN: Isa Zarewa: Tsohon sanata daga jihar Kano ya mutu a Abuja

Shehu Na'Allah Kura ne aka rantsar a matsayin kwamishinan kudi da habaka tattalin arziki inda Dr. Mohammed Tahir aka rantsar dashi a matsayin kwamishinan al'amuran addinin musulunci.

Dr. Zahara'u itace kwamishinan harkokin mata sai Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne aka rantsar a matsayin mai jagorantar ma'aikatar lafiya ta jihar. Sadiq Aminu Wali ne kwamishinan ruwa sai Mohammed Bappa Takai a matsayin kwamishinan kimiyya da fasaha.

Kabiru Ado Lakwaya ne kwamishinan matasa da wasanni sai Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ce babbar kwamishinan ilimi. Ibrahim Ahmed Karaye ne kwamishinan al'adu da bude ido sai Mukhtar Ishaq Yakasai ne kwamishinan aiyuka na musamman.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antu ta samu Mahmoud Muhammed a matsayin kwamishina sai Muhammaed Sunusi Saidu ya zama kwamsihinan ilimi. Ma'aikatar sufuri da gidaje ta samu jagorancin Barrister Lawan Abdullahi Musa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng