Abba Ya Aika Wa Majalisar Kano Muhimmiyar Buƙata, Zai Kafa Sababbin Ma’aikatu
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika wa majalisar jihar Kano bukatar kafa sababbin ma'aikatu guda hudu domin ci gaban jihar
- Ma'aikatun ayyukan jin kai, wutar lantarki da makamashi, tsaron cikin gida, da kuma ma’adanai su ne Abba ke so a kirkira
- Yusuf ya kuma mika sunayen mutane hudu ga majalisar domin tantance su a matsayin mambobi a majalisar zartarwa ta jiha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya rubutawa majalisar dokokin jihar takardar neman amincewar kafa sababbin ma’aikatu hudu.
Jerin ma'aikatun da Abba zai kirkira
Gwamnan, a cikin wasikar da kakakin majalisar Jibrin Falgore ya karanta, ya nemi a amincewar kafa sabbin ma’aikatun domin ci gaban jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Falgore ya ce ma’aikatun da ake son a samar sun hada da ma'aikatar ayyukan jin kai, wutar lantarki da makamashi, tsaron cikin gida, da kuma ma’adanai.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kuma bukaci amincewar majalisar wajen rusa shuwagabannin hukumar majalisar jihar da nada sabbin mambobi.
Abba zai nada sabbin kwamishinoni
Sababbin mambobin za su hada da tsohon kakakin majalisar, Gambo Sallau a matsayin shugaba, Zubairu Mamuda, Al’asan Kibiya, Ali Bala da kuma Halima Uba Jalli.
Sauran sun hada da Surajo Danbatta, Yahaya Rogo, Abubakar Dala da Garba Tsanyawa.
Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa Yusuf ya mika sunayen mutane hudu ga majalisar domin tantance su a matsayin kwamishinoni.
Wadanda mika sunayensu domin nadin sune Adamu Kibiya, Abdujjabbar Garko, Shehu Karaye da Mustafa Rabi’u-Kwankwaso.
Abba ya nada dan Rabiu Kwankwaso?
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamn Abba Yusuf, ya zabi dan ubangidansa a siyasa kuma tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso, a matsayin kwamishina.
Yusuf ya gabatar da sunan Mustapha Kwankwaso da wasu mutane uku a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Talata domin tantance su a matsayin mambobin majalisarsa.
Tsohon kwamishinan filaye da tsare-tsare, Adamu Aliyu, wanda aka kora a watan Satumba saboda ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun zaben jihar na cikin wadanda aka zaba.
Asali: Legit.ng