Kano: Abba Kabir Ya Tura Sunan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 Majalisa Domin Tantancewa
- Yayin da ya shafe kusan watanni 10 kan mulki, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya tura sunayen mutane hudu Majalisar jihar
- Gwamna ya tura sunayen nasu ne domin tantance su a matsayin karin kwamishinoni a jihar kan wadanda ake da su
- Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren kafar sadarwa ta zamani kan wannan nadi da ake shirin yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake tura sunayen mutane hudu Majalisar dokokin jihar domin tantance su.
Mai girma Abba Yusuf ya tura sunayen zuwa Majalisar ne domin tantance su a matsayin ƙarin kwamishinoni a jihar.
Wasu sunaye Abba ya tura Majalisar Kano?
Daga cikin wadanda aka tura akwai ɗan tsohon gwamnan jihar, sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai suna Mustapha Rabiu Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda ake so a nada cikin kwamishinoni sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Usman Shehu Aliyu da kuma Abduljabbar Garko.
Dalilin dakatar da kwamishina a Kano
Daga cikinsu akwai Adamu Aliyu Kibiya wanda shi ne aka dakatar kafin yanke hukuncin zaben jihar saboda katoɓarar da ya yi ga alkalan kotu.
Kibiya ya yi barazanar inda ya ke zargin akwai kullalliya cewa an ba alkakan kudi za su yi hukuncin da bai dace ba.
Daga bisani gwamnan jihar ya dakatar da shi bayan korafe-korafe daga jama'a wanda ake ganin barazana ce ga zaman lafiyar jihar.
A kwanakin baya, gwamnan ya ba kwamishinonin wa'adin kwanaki da su rubuto ayyukan da suka yi a ma'aikatunsu domin sanin makomarsu a gwamnati.
Mustafa Kwankwaso ya cancanta?
Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren kafar sadarwa ta zamani kan wannan nadi.
Salisu Yahaya Hotoro ya ce babu batun cece-kuce kan wannan saboda ɗan Kwankwaso shi ma ɗan kasa ne kuma ya na da gogewa da zai rike kowane mukami.
"Ɗan Kwankwaso shi ba ɗan jihar Kano ba ne? Shin akwai wata doka da ta ce shi ba zai rike wani mukami ba?
(Mustafa Kwankwaso) ya yi karatu ya na da gogewa na rike dukkan mukamin da aka ba shi."
"Bayan haka ba yau ya shiga siyasa ba duk kamfe da shi muka yi a kananan hukumomi 44, ya ba da dukkan gudunmawa."
- Salisu Yahaya Hotoro
Hotoro ya ce shi bai ga abin cece-kuce kan wannan lamari ba, ko da kuwa Rabiu Kwankwaso ne ya tura sunansa ai hidimar da ya yi wa jihar Kano da NNPP ya cancanci a ba shi kowace irin kujera.
Abba Kabir ya tausayawa wasu ƙauyuka
A baya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ɗauki ga wasu ƙauyukan jihar kan rashin ruwan sha.
Ƙauyukan sun hada da Danya da Kyallin Bula wadanda suka dade cikin halin matsin rashin ruwan sha a ƙaramar hukumar Bichi.
Ƙauyukan sun shafe shekaru a wahala sakamakon wuyar da suke sha wajen samun ruwan da za su yi amfani da shi.
Asali: Legit.ng