Babbar Kotun Kano Ta Yanke Wa Ɗan China Hukunci Kan Kisan Ummita, Ta Faɗi Dalili 1

Babbar Kotun Kano Ta Yanke Wa Ɗan China Hukunci Kan Kisan Ummita, Ta Faɗi Dalili 1

  • A ƙarshe, babbar kotun Kano ta yanke hukunci kan ɗan Sin da ake zargi da kisan Ummita bayan tsawon lokaci ana shari'a
  • Mai shari'a Sanusi Ado Ma’aji ya kama Mista Quandong Geng, ɗan kasar Sin da laifin kisan kai, bisa haka ya yanke masa hukuncin kisa
  • A watan Satumba, 2022 ne mutumin kasar wajen a ya kutsa kai gidan su Ummita kuma ya burma mata wuƙa har lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Bayan tsawon lokaci, babbar kotun jihar Kano mai zama a titin Miller a Bompai ta kawo ƙarshen shari'ar kisan Ummulkusum Sani Buhari wacce aka fi sani da Ummita.

Mai shari'a Sanusi Ado Ma’aji ya kama wanda ake zargi ɗan asalin ƙasar China, Quandong Geng, da laifin kisan budurwarsa, marigayya Ummita.

Kara karanta wannan

Sojoji za su sako mutum 200 da aka kama bisa zargin ta'addanci, za a mayar da su jihar Arewa

Quandong Geng da Ummita.
Ummita: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa Hoto: www.dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan ya gamsu da cewa ɗan China ne ya aikata kisan, Alkalin babbar kotun ya yanke masa hukuncin kisa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba ɗan China ya shiga gidan su Ummita a watan Satumba, 2022 kuma ya caccaka mata wuƙa har ta mutu.

A farko dai ya gudu daga gidan da ya aikata wannan ɗanyen aiki amma daga bisani dakarun ƴan sanda suka damke shi, rahoton Channels tv.

Yadda shari'ar ta gudana

A lokacin da ake yi masa tambayoyi a kotu, Ɗan China ya ce Ummita ta yaudare shi yayin da ta auri wani daban duk da suna soyayya kuma yana son ya aure ta.

Geng ya ce lokacin da suka fara shirye-shiryen aure, ya saya mata rigar amarya ta Naira miliyan ɗaya da rabi, sannan ya mata canjin sababbin kuɗi na N700,000.

Kara karanta wannan

Kano: Daina amfani da soshiyal midiya da wasu sharuɗa da kotu ta kafawa Murja Kunya

"Lokacin da ta kaini garinsu a Sokoto domin na gaisa da ƴan uwanta, na kashe N700,000 wajen yin alheri," in ji shi.

Ya ce Ummita ta yaudare shi bayan ya saya mata gidan N4m, motar N10m kuma ya ba ta N18m domin ta ja jarin kasuwanci.

Ya kara da cewa ya saya mata rigunan gwal da kudinsu ya kai N5m, ya bata N6m domin ta kammala karatu a jami’ar Sakkwato da kuma Naira miliyan daya na sa sola a gidansu.

Murja Kunya ta samu beli

A wani rahoton kuma Babbar Kotu a jihar Kano ta ba matashiyar 'yar TikTok , Murja Kunya beli kan kudi N500,000.

Kotun ta ba da belin ne da sharadin kawo mutum biyu da za su tsaya mata wanda daya dole zai kasance na kusa da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel