Hukumar NCC Ta Gurfanar da MTN a Gaban Kotu, an Gano Dalili

Hukumar NCC Ta Gurfanar da MTN a Gaban Kotu, an Gano Dalili

  • Hukumar kare hakkin mallaka ta Najeriya (NCC) ta gurfanar da kamfanin MTN da wasu mutum uku da kamfani daya a gaban kotu
  • Hukumar na tuhumar MTN da sauran hudu da aikata laifuffuka uku da suka shafi keta hakkin mallakar wani mawaki Maleke Idowu Moye
  • Ana zargin MTN ta yi amfani da wakoki da kide-kiden mawakin ba tare da izininsa ba, wanda ya saba dokar hakkin mallaka ta Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kare hakkin mallaka ta Najeriya (NCC) ta gurfanar da kamfanin MTN da wasu mutane uku da kamfani daya a gaban kotu.

Hukumar NCC ta gurfanar da kamfanin MTN gaban kotu
An yi karar kamfanin MTN kan laifuffukan take hakkin mallaka. Hoto: @copyrightngr, @MTNNG
Asali: Twitter

MTN da sauran wadanda aka gurfanar

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito, hukumar NCC shigar da ƙarar ne kan zargin MTN da sauran sun keta hakkin mallaka.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mutane uku da kamfani daya da ake tuhuma a gaban babbar kotun Abuja sun hada da; Karl Toriola, babban jami'in MTN, Nkeakam Abhulimen, Yahaya Maibe da Fun Mobile Ltd.

A tuhume-tuhume uku, hukumar NCC ta yi zargin cewa wadanda ake karar, tsakanin 2010 zuwa 2017, sun yi amfani da sautin kidan wakar wani Maleke Idowu Moye ba tare da yardarsa ba.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa MTN

Hukumar ta yi zargin cewa kamfanin MTN ya yi amfani da sautin wakar Maleke ta hanyar saka ta a matsayin "Caller Ring Back Tunes" ba tare da sahalewar mawakin ba.

Sautin wakokin Maleke da aka yi amfani da su sun hada da wakarsa ta 911, minimini-wanawana, Stop racism, Ewole, Low waist, No bother da Radio.

Ana zargin wadanda ake tuhumar da saka wa abokan huldarsu wadannan wakokin ba tare da izini ba, wanda ya keta hakkin mallakar mawakin.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun lalacewa Binance, Gwamnati ta yi karar kamfanin kan zargin laifuffuka 4

Dokar a kamfanin MTN ya taka

A tuhuma ta uku, ana zargin wadanda ake karar da mallaka da yin amfani da sautin waka ba bisa ka'ida ko neman izinin mawakin ba.

A cewar hukumar NCC, wadannan laifuffukan sun saba wa sashe na 20 (2) (a) (b) da (c) na dokar hakkin mallaka Cap. C28, da ke a kundin mulkin Najeriya, 2004.

Kamfanin labaran NAN ya ruwaito cewa ba a kai ga mika shari'ar ga wani alkali ba kuma ba a saka ranar fara sauraron shari'ar ba.

NCC za ta hana layin Glo kiran MTN

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce za ta dakatar da masu amfani da layukan Glo daga kiran layukan MTN.

Reuben Mouka, daraktan yada labarai na hukumar NCC ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar inda ya kamfanin Glo ya gaza biyan wasu kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.