Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fatattaki shugaban hukumar hakkin mallaka ta kasa, Tony Jaja

- An samu wannan labarin ne a wata takarda da kakakin ministan shari'a na kasa, Umar Gwanda, ya gabatar ranar Litinin

- Duk da takardar ta kunshi korar Jaja, amma bata sanar da wani dalili ba, hasali ma sai dai fatan alheri da samun nasara

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fatattaki shugaban hukumar hakkin mallaka, Tony Jaja, jaridar Punch ta wallafa.

An samu wannan labarin ne a wata takarda da kakakin ministan shari'a na kasa, Dr. Umar Gwanda, ya gabatar a ranar Litinin.

Babban sakataren ma'aikatar shari'a ta kasa, Dayo Apata (SAN), yasa hannu a takardar ranar 15 ga watan Oktoban 2020.

Takardar mai taken, "Takardar sallamarka daga matsayinka na shugaban hukumar zartarwa ta hakkin mallaka ta kasa", an gabatar da takardar a ranar 28 ga watan Satumba don nuna amincewar shugaban kasa akan sallamar Jaja.

Kamar yadda takardar ta nuna, an cire Jaja a ranar amma ba'a sanar da dalilin korarsa ba.

Takardar ta umarci tubabben shugaban da ya gabatar da duk wasu abubuwan gwamnati da ke hannunsa ga darekta Janar, John Asein.

Kamar yadda take rubuce a takardar, Antoni janar yayi masa fatan alheri da samun nasara a rayuwa.

KU KARANTA: Operation Murmushin Kada: 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon atisaye

Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka
Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

A wani labari na daban, fitacciyar kungiyar malaman jami'o'i ta ce har yanzu tana nan a kan bakanta, bata dakatar da yajin aikinta ba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar malaman reshen jihar Legas, Farfesa Olusiji Sowande, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2020.

Legeit.ng ta gano cewa, Sowande ya ce rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin sun dakatar da yajin aikin ba gaskiya bane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel