Gwamnati Ta Biya Maƙudan Kuɗin Fansa Wajen Ceto Ɗaliban Kaduna? Gwamna Sani Ya Faɗi Gaskiya

Gwamnati Ta Biya Maƙudan Kuɗin Fansa Wajen Ceto Ɗaliban Kaduna? Gwamna Sani Ya Faɗi Gaskiya

  • Malam Uba Sani ya bayyana cewa ko kaɗan cece-kuce kan batun biyan kuɗin fansa wajen ceto ɗaliban Kuriga ko akasin haka ba shi da amfani
  • Gwamnan ya ce mafi muhimmanci shi ne daliban sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya kuma gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta
  • A ranar Asabar da ta wuce ne hedkwatar tsaro ta sanar da cewa an ceto ɗaliban daga hannun ƴan bindiga cikin ƙoshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce jayayyar da ake ta yi kan zargin an biya kuɗin fansa wajen ceto ɗaliban Kuriga ba ta da muhimmanci.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan lamarin a cikin shirin 'siyasa a yau' na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta faɗi gaskiya kan biyan kuɗin fansa yayin ceto ɗaliban Kaduna

Malam Uba Sani.
Cece kuce kan batun biyan kuɗin fana bai da amfani, Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci shi ne gwamnati ta samu nasarar ceto dukkan ɗaliban da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba an sace yara ɗaliban makarantar firamare ta LEA da makarantar sakandiren gwamnati da ke Kuriga, kimanin makonni hudu da suka gabata.

Amma a ranar Asabar da ta gabata, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta sanar da cewa an ceto ɗaliban daga hannun ƴan bindiga.

Gwamnati ta biya kuɗin fansa kafin ceto ɗaliban?

Ana ta rade-radin cewa gwamnati ta biya kudin fansa ga masu garkuwa da mutane domin a sako yaran, lamarin da Uba Sani ya yi fatali da shi.

A rahoton Daily Trust, Gwamna Sani ya ce:

"Abin da ya fi muhimmanci a yau shi ne yaranmu sun dawo gida. Mafi yawan waɗannan raɗe-raɗin da ke yawo ba dole bane, idan ɗanka aka sace, za ka tsaya kana zargin ta ya aka ceto shi?

Kara karanta wannan

Bayan an kubutar da dalibai 137, Gwamna Uba Sani ya fadi hakikanin adadin daliban da aka sace

"Amma wasu mutane da ba su da wata alaka da lamarin, su ke fitowa da guna-gunin da bai kamata ba a kan ko an biya kudin fansa, wace hanya aka bi, mu abin da ke gabanmu a Kaduna shi ne yaranmu sun dawo gida.

Yadda aka kuɓutar da ɗaliban Kuriga

Malam Uba Sani ya ƙara da bayanin cewa gwamnati ta kula sosai wajen kokarin kubutar da ɗaliban cikin hikima.

"Mun yi iya ƙoƙarinmu don kada mu jefa rayuwar yaran da ba su ji ba ba su gani ba cikin haɗari. Wasu mutane sun yi ƙoƙarin siyasantar da lamarin gaba daya," in ji shi.

DHQ ta ayyana neman ƴan ta'adda 97

A wani rahoton kuma Hedkwatar tsaron Najeriya ta ayyana neman Simon Ekpa, shugaban tsagin IPOB da wasu mutane 96 ruwa a jallo kan zargin ta'addanci.

Jerin waɗanda ake neman ruwa a jallo ya ƙunshi sunaye da hotuna daga shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262