Gwamna Abba Ya Kai Dauki Ga Kauyukan da Suka Kwashe Shekaru Ba Ruwan Sha a Kano

Gwamna Abba Ya Kai Dauki Ga Kauyukan da Suka Kwashe Shekaru Ba Ruwan Sha a Kano

  • Gwamnan Kano ya kai ɗauki ga mutanen ƙauyukan Danya da Kyalƙin Bula a ƙaramar hukumar Bichi da ke jihar
  • Abba Kabir Yusuf ya unurci a gina musu rijiyoyi masu amfani da hasken rana domin magance matsalar rashin ruwan sha da suke fama da ita
  • Kauyukan dai sun samu wannan tallafin ne bayan wani rahoto ya bayyana irin wahalar da suke sha kafin samun ruwan amfanin yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki ga ƙauyukan Danya da Kyallin Bula da fama da matsalar rashin ruwan sha a ƙaramar hukumar Bichi ta jihar.

Ƙauyukan sun shafe shekaru a wahala sakamakon wuyar da suke sha wajen samun ruwan da za su yi amfanin yau da kullum da shi.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum 20, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

Gwamna Abba ya fara sabon aiki a Kano
Gwamna Abba Kabir ya umurci a gina rijiyoyi a kauyukan Danya da Kyallin Bula Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba ya ɗauki matakin kai musu ɗauki ne bayan wata hira da aka yi da su a makon da ya gabata, inda suka bayyana matsanancin halin da suke ciki na rashin ruwan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dattijo mai shekara 90 da aka zanta da shi a lokacin, ya bayyana cewa shi ma a haka ya taso ya ga iyayensa na shan wannan wahalar.

Ya yi nuni da cewa suna shafe kwanaki biyu zuwa uku bayan sun yi tafiyar sa'a uku domin samun ruwan sha a wani ɗan kogo.

Wane ɗauki Gwamna Abba ya kai musu?

Biyo bayan bayyanar rahoton halin da mutanen ƙauyen suke ciki, Gwamna Abba Kabir ya bada umurnin a gina musu rijiyoyi masu amfani da hasken rana domin samar da ruwan sha.

Dahir M. Hashim wanda gwamnan ya ba su aikin samar da rijiyoyin ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda yara ƙanana da ya kamata a ce suna makaranta suke kwana a kan layi domin samun ruwan sha.

Tuni har an fara aikin samar da rijiyoyin ga waɗannan ƙauyukan domin tsamo su daga halin da suke ciki.

Ramadan: Batun kashe N6bn a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya musanta batun cewa gwamnatinsa ta ware N6bn domin ciyarwa a watan azumin Ramadan.

Gwamnan ya yi nuni da cewa abin da gwamnatinsa ta ware domin gudanar da aikin ko N2bn bai kai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng