Tinubu Ya Yi Magana Kan Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna, Ya Sha Sabon Alwashi

Tinubu Ya Yi Magana Kan Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna, Ya Sha Sabon Alwashi

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi tsokaci game da ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su tare da malamansu a jihar Kaduna
  • A cewar shugaban ƙasan, ya kamata gwamnatocin jihohi da na tarayya da su riƙa yin aiki tare domin kare aukuwar irin hakan a nan gaba
  • Daga nan sai Tinubu ya jinjina wa sojojin Najeriya, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da duk wanda ke da hannu a aikin kuɓutar da yaran

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Aso Rock Villa, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi maraba da ceto ɗalibai 137 da sojojin Najeriya suka yi bayan an yi garkuwa da su a Kaduna a ranar Alhamis 7 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

Shugaban ƙasan ya yi maraba da kuɓutar da yaran ne a ne a cikin wata sanarwa a safiyar ranar Lahadi, 24 ga watan Maris 2024.

Tinubu ya yi murna kan ceto daliban Kaduna
Tinubu ya yaba da ceto daliban da aka sace a Kaduna Hoto: @OfficialABAT, @aonanuga1956
Asali: Twitter

A cikin saƙon nasa, Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa akwai buƙatar tabbatar da cewa makarantu sun zama wurare masu tsaro domin bayar da ilmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai ba Tinubu shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale.

Shugaba Tinubu ya yaba da ƙoƙari da jajircewar sojojin Najeriya, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da kuma mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Me Tinubu ya ce dangane da ceto ɗaliban?

Daga nan sai shugaban ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya, musamman a kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna Uba Sani ya bayyana babbar damuwarsa

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Shugaba Tinubu ya kuma yi maraba da sakin ɗaliban makarantar Tsangaya da ke jihar Sokoto, inda ya yaba wa dukkanin ɓangarorin da suka yi ƙoƙari hakan ta tabbata.
"Shugaban ƙasan ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa na samar da dabaru domin tabbatar da cewa makarantunmu sun zama wurin koyon ilmi cikin aminci ba wuraren sace-sacen mutane ba."

DHQ ta tabbatar da ceto ɗaliban Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta tabbatar da ceto ɗaliban da aka sace a jihar Kaduna.

DHQ ta ce jami'an tsaro sun ceto ɗaliban ne su 137 tare da haɗin gwiwar ƴan banga a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel