Yadda Karancin Wuta Ya Jefa Musulman Najeriya Ga Tsadar Kankara da Ruwan Leda

Yadda Karancin Wuta Ya Jefa Musulman Najeriya Ga Tsadar Kankara da Ruwan Leda

Jihar Kaduna - Wutar lantarki a Najeriya ta zama tamkar kuɗi a wajen talaka, kafin ya same ta sai ya wahala. A hannu ɗaya kuma gidajen ruwan leda sun kara kudin ruwa da kaso 130% a shekara ɗaya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Musulmi a watan Ramadan sun fi buƙatar wutar lantarki fiye da ko yaushe, saboda samun ruwan sanyi ko ƙanƙarar da za su sanyaya maƙoshi idan sun yi buɗa baki.

Rashin wadatacciyar wutar lantarki ya jawo farashin ledar ruwa mai sanyi ta lula zuwa N400, yayin da ƙanƙarar ruwa ta kullawa ta haura N500 a jihar Kaduna.

Ramadan: Farashin ruwan sanyi da ƙanƙara a Kaduna
Kaduna: Rashin wutar lantarki ya jawo farashin ruwan sanyi da ƙanƙara ya lula zuwa N500 a azumi
Asali: UGC

Legit Hausa ta gudanar da bincike domin gano halin da ƴan Najeriya musamman Musulmi suke ciki a watan Azumi ta fuskar rashin wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan, mun binciko yadda farashin ruwan leda da na kankara ya haura sama, musamman a wannan wata na Ramadan mai alfarma ga musulmi.

Matsalar wutar lantarki a Kaduna

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin wutar lantarki, wannan ya jawo durkushewar kananan kamfanoni da dama.

Lokuta da dama kamfanin wutar lantarki na Kaduna na fitar da sanarwar yankunan da suka sami matsalar wutar, da kuma matakin da suka dauka don magance hakan.

Kamfanin na amfani da shafukansa na sada zumunta domin fitar da irin wannan sanarwar kamar wannan sanarwar da kuma wannan da ke ƙasa:

Tsadar ƙanƙarar ruwan ƙullawa

Saboda rashin wutar lantarki, gidaje ko mutanen da ke sarrafa ƙanƙarar ruwa musamman a lokutan azumi, sun ƙara kudin kankarar zuwa N600 duk guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Kungiya ta yi magana kan zargin da ake yi wa ministsn Tinubu na ba 'yan bindiga tallafin abinci

A azumin da ya gabata na 1444, ana sayar da ƙanƙarar kullawa a kan N300, kenan an samu karin kaso 50% a cikin shekara daya.

Malam Haruna Hayin Dan Mani, Rigasa, Kaduna, wanda ya zanta da wakilin Legit Hausa, ya ce ƙarin kuɗin ya faru ne sakamakon rashin wutar lantarki.

Haruna ya ce:

"Yanzu ni ka ga sai nayi amfani da gas na N12,000 a kullum nake samar da ƙanƙarar nan, tun asuba idan na kunna inji sai bayan an sha ruwa nake kashewa.
"Azumin da ya gabata, ina ga gas din bai wuce N800 lita ba, amma yau muna sayensa a kan N1550 a gidajen mai na gwamnati. Dole mu ƙara kudin mu ma."

Me ya jawo tsadar ruwan leda?

A azumin 1444, gidajen ruwa suna sayar da jaka ɗaya akan N70, amma a wannan azumin, kudin ya haura zuwa N200. Tambayar ita ce, me ya jawo hakan?

Salim Isah, manajan gidan ruwan Dantafiya Table Water da ke Hayin Rigasa, ya shaidawa wakilinmu cewa:

Kara karanta wannan

Lalacewar wutar lantarki: TCN ta yi aiki tukuru, ta gyara matsalar wuta da aka shiga a Najeriya

"Shekarar da ta wuce muna sayen ledar jera ruwan a kan N4000, amma yanzu ta koma N13,000. Ledar ruwan kanta ta koma N3,700 duk 1kg sabanin N800.
"Sannan ka duba yadda fetur ya yi tsada, ga babu wutar lantarki. Abin lura a nan, gidajen ruwa na kokari sosai, tsadar kayan tana wajen shagunan da ke sayarwa daya daya."

Binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewa ana sayar da ledar ruwa a cikin anguwanni akan N400, yayin da ake sayar da ƙwara uku akan N50.

Ra'ayin jama'a kan tsadar ruwa da kankara

Wani ɗan unguwar Sanusi, jihar Kaduna, wanda ya bayyana sunansa da Kabir, ya ce ya hakura da sayen ƙanƙara a azumin nan saboda tsadar da ta yi.

Kabir ya ce ana sayar da ƙanƙara N700 babba, ƙarama kuma N400, sai ta ledar ruwa akan N50, yayin da shi ruwan sanyi ya koma zuwa N30 a unguwar Sanusi.

Kara karanta wannan

An kashe manyan hatsabiban ƴan bindiga 2 da suka addabi bayin Allah a jihar Arewa

Daga yankin Unguwar Mu'azu kuwa, Yusuf Gwalmi, ya shaida mana cewa yaran da ke sayar da ƙanƙara a unguwar na cin karensu ba babbaka.

"Kankara yanzu N700 saye ko bari, wata za ka ga ta fara komawa ruwa, an yi maka sauki ka bayar da N500. Na ga shagon da aka sayar da kankarar pure water N100, saboda don zuciya."

- A cewar Gwalmi.

Mutane da dama sun tafi akan cewa rashin wutar lantarki ne ya jawo tashin kudin kankara, yayin da man fetur da karin kudin leda ya jawo tashin kudin ruwan leda.

Gidaje da dama na da firinjin da zai iya saka ruwa yayi kankara, amma saboda rashin wutar, sukan koma hoto kawai.

Da ace wutar lantarki za ta tsaya, to da gidaje da dama sun iya sarrafa ruwan sanyi ko ƙanƙarar da za su yi amfani da ita, da hakan ya rage farashin kudin kankarar da na ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Sanata ya dauki zafi kan karin kudin kujera, ya fadawa Tinubu abin da zai yi

Mutane 12 da zasu iya shan azumi

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa akwai mutane 12 da addini ya yarje masu su sha azumi a lokacin watan Ramadan.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya yi cikakken bayani a kan wadannan mutane, ya kuma yi nuni da cewa wasu za su rama wasu kuma ba za su rama azumin da suka sha ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.