Da duminsa: Masu Kamfanonin Pure Water a Abuja sun sanar da sabon farashi, N20 daga yanzu

Da duminsa: Masu Kamfanonin Pure Water a Abuja sun sanar da sabon farashi, N20 daga yanzu

  • An kara farashin ruwan leda a birnin tarayya Abuja
  • Wannan ya biyo bayan gargadi da barazanar da masu ruwan Nasarawa suka yi
  • Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan sabon labari

Abuja - Kungiyar masu masana'antun ruwan leda a birnin tarayya Abuja sun sanar karin Farashin ruwa sakamakon hauhawar da farashin abubuwa da keyi a fadin tarayya.

Sabosa rashin ingantacce da tsaftaccen ruwa sha, yan Najeriya sun dogara da Shan ruwan Leda wanda akafi sani da 'Pure Water'.

A baya ana sayar da Ledan 'Pure Water' N10 amma yanzu sun sanar da cewa za'a koma sayarwa N20.

Masu masana'antun sun bayyana cewa dole ce ta sa sukayi wannan kari saboda hauhawar kayan sarrafan ruwan.

Jaridar Premium Times ta ji daga bakin Shugaban kungiyar na Abuja, Mohammed Akwuh, inda yace mambobin kungiyar an yi ittifakin sabon farashin ne ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Yace wannan sabon farashin zai shafi jihohin dake makwabtaka da Abuja irinsu Neja da Nasarawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Lallai mun kara farahin ruwa a Abuja. Farashin kayayyaki sun tashi yanzu. Mun ganawa sau da dama a watanni biyu da suka gabata kuma mun yanke shawara ranar Asabar.

Da duminsa: Masu Kamfanonin Pure Water a Abuja sun sanar da sabon farashi, N20 daga yanzu
Da duminsa: Masu Kamfanonin Pure Water a Abuja sun sanar da sabon farashi, N20 daga yanzu
Asali: Facebook

Ana sa ran za'a fara sayar leda daya N20

Yanzu kamfanonin ruwa zasu fara sayard a jaka daya tsakanin N180 da N200 dangane da adadin da mutum ya saya. Yan kasuwa kuma zasu fara sayarwa N240.

A jawabin da kungiyar ta saki ranar Alhamis, tace:

"Masu kamfanonin ruwa zasu rika sayar da jaka kasa da guda 100 a farashin N200/jaka."
"Idan kuma mutum zai saya jakunkuna 100 da abinda yayi sama, N180 za sayar da kowani daya. Yan kasuwa masu sayar mai sanyi kuma zasu rika sayarwa N240."

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Gabanin wannan kari, ana sayar da jaka daya N120.

Zamu fara sayar da 'Pure Water' N20: Masana'antun ruwa a jihar Nasarawa

Kungiyar masu masana'antun sarrafa ruwan sha na leda da gora, shiyar jihar Nasarawa ta ce mambobinta zasu fara sayar da ledan Fiya-wata N20 nan da kwanaki.

Shugaban kungiyar na Keffi-Mararaba, Usman Diggi, ya bayyana hakan ne ranar Asabar bayan taron karawa juna ilimi da akayiwa mambobin kungiyar a karamar hukumar Karu ta jihar.

Ya ce kungiyar ta yanke shawaran haka ne saboda kayan sarrafa ruwa sun yi tsada kuma ba zai yiwu su cigaba da sayar da ruwan leda N10 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng