Ramadana: Yadda kankara ta zama kamar nama a Kano saboda tsananin zafi

Ramadana: Yadda kankara ta zama kamar nama a Kano saboda tsananin zafi

  • Dillalan kankara na ci gaba da cin duniyarsu da tsinke a jihar Kano yayin da zafi ke kara tsananta a Ramadana
  • Hakazalika, farashin kankara na tashi a jihar saboda matsalar wutar lantarki da aka samu cikin kwanakin nan
  • Hira da kwastomomi da masu sayar da kankara ya bayyana yadda kasuwar kankara ke kawo romon riba mai yawa

Jihar Kano - Wani rahoton Vanguard ya ce, masu sayar da kankarar ruwa na ci gaba da cin ribar kasuwanci a Kano sakamakon tsananin zafi da ake fama da shi a yankin a lokacin azumin watan Ramadan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa daurin kankara daya yana kai farashin N150 zuwa sama, ya danganta da girmansa da wurin da ake sayar da shi.

Kara karanta wannan

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

Yadda jama'a suka zama masoya kankara a Ramadana a Kano
Ramadana: Yadda kankara ta zama kamar nama a Kano saboda tsananin zafi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

NAN ta lura cewa hasashen yanayi a Kano yana kai dangon zafi 40° zuwa 43° na ma'aunin Celsius zuwa sama, da tsakar rana, tun lokacin da aka fara azumi.

Galibi masu sayar da kankara suna adana shi a cikin buhuna ne ko manyan robobi domin hana shi narkewa cikin sauki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu sayar da kankaran, wadanda galibinsu matasa maza da mata ne, su kan fara sayar da kankarar ne daga karfe hudu na yamma kullum a kan tituna daban-daban a cikin birnin Kano.

Irin ribar da 'yan kankara ke samu

Wani mai sayar da kankara mai suna Abdullahi Yusuf ya ce a kullum yana samun makudan kudade.

Ya ci gaba da cewa, suna samun karin masu saye idan aka samu matsalar wutar lantarki, saboda yawancin mutane kan garzayo domin sayen kankarar buda baki.

Wata mai sayar da kankara, Misis Patience Christopher, ta ce ta kan samu yawaitar ciniki a lokacin bazara.

Kara karanta wannan

Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF

Ta kara da cewa suna samun karin kudade daga sana’ar a lokacin azumin Ramadan, musamman ma lokacin zafi.

Martanin wani kwastoma kan shan ruwan sanyi a Azumi

A nasa bangaren, wani kwastoma, Aliyu Nura, ya ce a kullum yana sayen kankara ta Naira 400 zuwa 500 ga iyalansa.

Nura ya ce da zarar rana ta fadi ana bukatar a sha ruwan sanyi kafin a ci komai saboda tsananin zafi.

Ya kara da cewa masu sayar da kankara kan kara farashin su ne idan aka samu matsalar wutar lantarki a garin sakamakon yawan bukatar kankara da ake samu, kuma galibin jama’a ba sa iya amfani da janareta wajen samar da wutar lantarki mai karfi.

A cewarsa:

"Sun dogara ga masu sayar da kankara don samun kayan da za su shirya ruwan sanyi don buda baki."

Matsalar wutar lantarki a Kano

NAN ta rahoto cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) ya bayyana cewa matsalar wutar lantarki a halin yanzu na faruwa ne sakamakon rugujewar turken wuta da aka yi a na’urar lantarki ta kasa.

Kara karanta wannan

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

Madam Hauwa Shuaibu, wacce ta sanya hannu a sanarwar a madadin shugabar harkokin sadarwa na kamfanin KEDCO, ta nemi afuwar abokan huldarsu kan lamarin, kamar yadda Gazette ta ruwaito.

Ta kuma ba su tabbacin samun ingantaccen wutar lantarki da zarar lamarin ya daidaita.

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel