Buhari Ya Shiga Jimami Yayin da Hadiminsa Ya Tafka Babban Rashi a Rayuwarsa
- Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kadu bayan rasuwar matar hadiminsa a bangaren daukar hoto a Abuja
- Hadimin nasa, Sunday Aghaeze ya rasa matarsa mai suna Mabel a farkon watan Maris inda aka binne ta a ranar Asabar
- Buhari a cikin sakon ta’aziya da ya fitar ya tura sakon jaje inda ya ce tabbas iyalan Aghaeze sun tafka babbar rashi na uwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi babban rashi bayan rasuwar matarsa.
Tsohon hadimin wanda ya ke daukar Buhari hoto, Sunday Aghaeze ya rasa matar tasa ce mai suna Mabel Odion Aghaeze a farkon watan Maris.
Yaushe matar hadimin Buhari ta rasu?
Aghaeze shi ya bayyana mutuwar matar tasa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 23 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na shiga mummunan yanayi da duhu da kuma hawaye na rashin matar kirki Mabel.”
- Sunday Aghaeze
Duk da ba a tabbatar da silar mutuwar tata ba tuni aka binne ta a ranar Juma’a 22 ga watan Maris a Abuja.
Sakon jaje da Buhari ya tura
Buhari a cikin sakon ta’aziya a ranar Asabar 23 ga watan Maris, ya jajantawa Aghaeze kan wannan babbar rashi.
Sakon ta’aziyar na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a karshen mako.
“Iyalan Aghaeze sun tafka babban rashi wacce ta kasance uwa ta gari kuma mai son zaman lafiya da kaunar mutane.”
- Muhammadu Buhari
Buhari ya bukaci Aghaeze da ‘ya’yansa da su dauki kaddara kan wannan babbar rashi da suka yi na rashin mahaifiya kuma uwa ta gari.
A shekarar 2016 Buhari ya nada Aghaeze a matsayin mai daukar hoto inda ya sake nada shi a shekarar 2019, cewar Leadership
Mawaki a Najeriya ya rasu
A baya, kun ji cewa shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 77 a duniya.
Marigayin da aka fi sani da 'Kabaka' ya shahara a wakoki inda ya shafe fiye da shekaru 20 ya na waka kafin rasuwarsa.
Asali: Legit.ng