Kaduna: An Ceto Daliban Makaranta 137 da ‘Yan Bindiga Suka Dauke Bayan Kwana 16
- Daliban makarantar Kuriga da aka yi garkuwa da su sun kubuta kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sanarwa
- Gwamna Uba Sani ya shaida haka a safiyar Lahadi, sai dai bai yi cikakken bayanin yadda ‘yan makarantar suka tsira ba
- Jawabin Mai girma cike yake da yabon Bola Tinubu da Nuhu Ribadu yayin da yaran suka tsira daga hannun ‘yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Daliban Kuriga sun bar hannun 'yan bindiga
Kaduna – Daliban makarantar Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci.
‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wadannan yara sun fito da su kamar yadda hukuma ta tabbatar a yau Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uba Sani ya sanar da ceto yaran Kuriga
Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ba da wannan sanarwa a shafukansa na sadarwa da safiyar nan.
Malam Uba Sani a jawabin da ya fitar a shafin Facebook, ya fara da sunan wa Allah SWT wajen sanar da nasarar.
Mai girma gwamna ya yi wa Bola Ahmed Tinubu, GCFR godiya ganin yadda ya ba da fifiko wajen ganin an ceto yaran.
Gwamna Uba Sani ya ce Mai girma shugaban kasa ya yi tsayin-daka wajen ganin an ceto yaran babu ko da kwarzane.
Kuriga: Bangaren jawabin Gwamnan Kaduna
"A lokacin da yaran suke tsare, na yi magana da Shugaban kasa sau da-dama.
(Tinubu) ya taya mu takaici, ya taya mu jaje kuma ya yi aiki dare da rana domin ganin daliban sun dawo."
- Uba Sani
Ribadu da Sojoji sun taka rawar gani
Jawabin gwamnan ya kunshi ambato na musamman ga Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Uba Sani ya ce sun shafe darare babu barci tare da Malam Nuhu Ribadu saboda a ga yadda za a ceto ‘yan makarantar.
Har ila yau, Sanata Sani ya ce dole a jinjinawa sojoji da suka nuna rashin tsaro da jajircewa wajen kubutar da yaran.
A karshe gwamnatin Kaduna ta yi godiya ga al’ummar Najeriya da suka dage da addu’a har aka ga rana irin ta yau.
Atiku ya koka kan matsalar tsaro
Ana da labari cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah wadai kan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan a yau.
Jagoran adawar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna yatsa ga Bola Tinubu bayan kashe mutane a Neja.
Asali: Legit.ng