'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa da Mutane a Kaduna

'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa da Mutane a Kaduna

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun daƙile wani mugun nufi da ƴan bindiga suka yi a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna
  • Ƴan sandan sun daƙile wani yunƙuri da miyagun suka yi na yin garkuwa da mutane a kan babbar hanyar
  • A yayin artabun da suka yi, jami'an tsaron sun fatattaki tsagerun tare da raunata da dama daga cikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Mansur Hassan ya fitar a ranar Juma'a, 22 ga watan Maris 2024, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga
'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami'an ƴan sandan sun daƙile harin ne a yayin da suke gudanar da aikin sintiri na yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya ce ƴan sandan sun yi artabu da ƴan bindigan ne, wanda hakan ya tilasta musu tserewa, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Yadda ƴan sanda suka fafata da ƴan bindigan

A kalamansa:

"A ranar 21 ga watan Maris, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jami’an 47PMF da ke ofishin ƴan sanda na Buruku sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane da ƴan bindiga suka yi a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna.
"Yayin da suke gudanar da sintiri na hana aikata laifuka a kan babbar hanyar, jami’an ƴan sandan na PMF sun yi arba da ƴan bindiga a kusa da kwanar Ugara, inda ƴan bindigan suka buɗe musu wuta bayan sun hango su.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kawo hanyar magance matsalar 'yan bindiga cikin sauki

"Cikin nuna jajircewa da ƙwarewa, jami’an na PMF sun mayar da martani, tare da daƙile barazanar ƴan bindigan.
"Musayen wutan da aka yi ya tilasta wa ƴan bindigar tserewa cikin daji
"Duk da ƙoƙarin da suka yi na gujewa faɗawa hannun jami'an tsaro, ƴan bindigan sun samu munanan raunuka yayin arangamar."

Hassan ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Audi Ali, ya yabawa ‘yan sandan bisa jajircewarsu da kuma ɗaukar matakin gaggawa wajen daƙile lamarin.

Ya ce kwamishinan ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton abin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.

Ɗaliban Sokoto sun kuɓuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaliban makarantar tsangaya da aka sace a jihar Sokoto, sun kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.

Ɗaliban sun shaƙi iskar ƴanci ne bayan sun kwashe kwanaki a tsare a hannun miyagun ƴan bindigan da suka sace su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng