Ana Sa Ran Naira Za Ta Mike, CBN Ya Biya Bashin Dala Biliyan 7 da Emefiele Ya Bari

Ana Sa Ran Naira Za Ta Mike, CBN Ya Biya Bashin Dala Biliyan 7 da Emefiele Ya Bari

  • A kokarin farfaɗo da darajar naira a Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauki hanyar kawo karshen matsalar
  • Bankin karkashin jagorancin Yemi Cardoso ya biya bashin $7bn da ya gada daga tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele
  • Legit Hausa ta ji ta bakin malami kuma masanin tattalin arziki kan wannan mataki na bankin CBN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ta biya bashin $7bn da gwamnan bankin, Yemi Cardoso ya gada bayan shigarsa ofis a 2023.

Darektar yada labaran bankin, Hakama Sidi Ali ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Akwai alamun samun sauƙi, darajar Naira ta lula zuwa N1400/$1 a kasuwar canji

CBN zai daga darajar naira bayan biyan basukan $7bn da Emefiele ya ciyo
Bankin CBN ya biya basukan Dala $7bn da Emefiele ya tara. Hoto: Central Bank Of Nigeria.
Asali: UGC

Wane amfani biyan bashin Dalan zai yi?

Hakama ta tabbatar da biyan dukkan basukan wanda ake ganin zai iya saka darajar naira ta tashi a kasuwar duniya, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce bankin ya dauki wani kamfanin kula da kudi mai suna Deloitte Consulting da zai tabbatar da biyan bashin ga wadanda suka cancanta kadai.

"Duk wata harkar cinikayya da ba ta cancanta ba an tura ta zuwa hukumomin da suka dace domin bincike."

- Hakama Sidi Ali

A bangare daya, gwamnan bankin CBN, Yemi Cardoso ya bayyana amfanin biyan bashin domin inganta naira, cewar Channels TV.

CBN ya fadi muhimmancin biyan bashin Dala

"Mun dauki wannan biyan basukan da muhimmanci domin tabbatar da ɗaga darajar naira a Najeriya."

- Yemi Cardoso

Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ke dauka domin tabbatar da inganta darajar naira a kasar.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta bankaɗo kura-kurai a bashin N30tn da CBN ya ba gwamnatin Buhari

Legit Hausa ta ji ta bakin malami kuma masanin tattalin arziki kan wannan mataki na bankin CBN

Lamia Bello ya ce hakan zai taimaka wurin ba naira kariya, sai dai ya ce ba zai tasiri wurin inganta tattalin arziki ba.

"Tabbas ya yi kokari kuma hakan zai sanya wa naira kariya to amma zancen zai rage hauhawar farashin dala wannan ba zai yi wani tasiri babba ba."
"Muddin CBN na son sauko da dala dole ya bi hanyoyin gyara matatun mai domin rage daukar daloli zuwa siyo taceccen mai.
"Na biyu, samar da abubuwan sarrafa kayayyaki da kamfanoni ke bukata a cikin gida da kuma sanyawa dala ido a kasuwa."

- Lamido Bello

CBN zai kori darektoci 7 daga aiki

A baya, mun ruwaito muku cewa Babban Bankin Najeriya, CBN na shirin korar darektoci 19 daga aiki nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Tunji-Ojo: Badakalar Betta Edu da wasu zarge-zarge 2 da ake yi wa ministan Tinubu

Rahotanni sun tabbatar cewa CBN na shirin korar manyan ma'aikata daga aiki biyo bayan sallamar daraktoci bakwai da bankin ya yi a makon da ya gabata.

Wannan nuna zuwa ne yayin da darajar naira ke faman durkushewa musamman a wannan matsi na tattalin arziki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.