Sace Dalibai: Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Babbar Damuwarsa
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi taron gaggawa da masu ruwa da tsaki kan matsalar rashin tsaro
- Uba Sani ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun yawaitar masu ba ƴan bindiga bayanai a ƙauyukan da ke fama da matsalar
- Ya umurci sarakunan gargajiya na yankunan da su tabbatar sun zaƙulo waɗannan miyagun domin miƙa su a hannun jami'an tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wani taron gaggawa da shugabannin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomi masu fama da matsalar tsaro a Kaduna ta Tsakiya.
Gwamna Uba Sani ya kira taron ne a ranar Laraba, 20 ga watan Maris 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.
Sake dawowar ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da mutane shi ne batun da ya mamaye taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaman ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi bakwai na Chikun, Birnin Gwari, Kajuru, Igabi, Kachia, da Kagarko.
Ana ƙoƙarin ceto dalibai 287
Gwamnan, wanda ya ce ana ƙoƙarin kubutar da ɗalibai 287 da aka sace a Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun, ya nuna damuwarsa kan ƙaruwar masu ba ƴan bindiga bayanai, a cikin ƙauyukan, inda ya yi alƙawarin ganowa tare da cafke su.
Uba Sani ya shaidawa mahalarta taron cewa ya samu tabbaci daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, cewa za a kuɓutar ɗaliban.
Wace buƙata Uba Sani ya nema?
Sai dai ya bukaci shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya, da su kai rahoton duk wata baƙuwar fuska a cikin al’ummarsu ga jami’an tsaro, domin daƙile ayyukan masu ba ƴan bindiga bayanai, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
A kalamansa:
"Batun tsaro ya shafi kowa da kowa kuma mun yi imanin cewa sarakunan gargajiya suna da nauyi mai yawa wajen taimakawa jami’an tsaro, musamman tabbatar da cewa an gano duk wasu baƙin da suka shigo cikin al’umma.
"Muna zargin cewa wasu daga cikinsu masu ba da bayanai ne kuma a yau na umarci sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomi da su zaƙulo waɗannan baƙin mutanen tare da kai rahoto ga jami’an tsaro cikin gaggawa."
An ceto mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mutum 16 da aka sace a jihar Kaduna.
Rundunar ta yi nasarar ceto su ne a hannun ƴan bindiga a ƙauyen Tantatu da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar.
Asali: Legit.ng