Majalisa Ta Amince da Ƙarin Albashi Ga Alƙalan Najeriya, an Samu Cikakken Bayani
- Majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar karawa babban joji na ƙasa da alkalan kotunan Najeriya albashi
- Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya gabatar da bukatar ƙarin albashin alkalan da ma'aikatan shari'a ga majalisar
- Idan Tinubu ya rattaba hannu kan dokar, baban joji na ƙasa zai riƙa samun albashi da alawus na kusan N60m a shekara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta amince da sabuwar dokar ƙarin albashi da alawus ga babban joji na ƙasa (CJN) da sauran alƙalan kotunan Najeriya.
Tribune Online ta ruwaito cewa idan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar, babban joji na ƙasa zai riƙa samun albashi da alawus na N64m a kowacce shekara.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar tarayya bukatar ƙarin albashi ga alkalai da ma'aikatan shari'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sabon albashin alƙalan Najeriya:
Albashi Alkalin Alkalai na ƙasa (CJN)
A yanzu babban joji na ƙasa (CJN) zai riƙa ɗaukar albashin N1,121,884.83 a kowanne wata.
Akwai kuma alawus na N4,263,162.35 a kowanne wata da alawus din N6,731,308.98 wanda zai riƙa samu akai akai.
A yayin da ya kai matakin ritaya kuwa, zai samu giratuti na N80,775,707.70, da bashin mallakar mota na N53,850,471.80
Albashin Alƙalan Kotun Ƙoli
A cewar rahoton Premium Times, alƙalan Kotun Ƙoli za su rika daukar albashin N826,116.19 a kowane wata da alawus na N4,213,192.
Akwai alawus na hayar gida na N9,913,394.22 da kuma giratuti na N29,740,182.65 idan sun yi ritaya.
Akwai alawus na kayan gida da na bashin mota da ya kai N39,653,576.88.
Albashin alƙalan Kotun Daukaka Kara
A yanzu alkalan Kotun Daukaka Kara za su rika samun albashin N665,475.97 a kowanne wata, da alawus din N3,726,665.40 na wata wata.
Akwai alawus na hayar gida da ya kai N7,985,711.58 da kuma N23,957,134.74 a matsayin kudin giratuti idan sun yi ritaya.
Za ba su N31,942,846.32 a matsayin lamunin sayen mota da kudin gyaran gida.
Albashin Alƙalan babbar kotun tarayya
Alkalan da ke a wannan rukunin su ne:
Alkalan babbar kotun tarayya, kotun masana'antu, babbar kotun Abuja, kotun shari'a ta daukaka kara, kotun kwastomare ta Abuja.
Sauran su ne alkalan babbar kotun jiha, kotun shari'a ta jiha, kotun kwastomare ta jiha; dukan su suna daukar albashi iri ɗaya ne.
Duka alkalan wadannan kotuna na sama za su rika samun albashin N665,475.97 a kowanne wata.
Akwai alawus na N3,572,022.61 a kowanne wata da giratutin N23,957,134.74 idan sun yi ritaya.
Cin hanci: Alkalin Alkalai ya gargaɗi alƙalai
A wani labarin, Babban joji na ƙasa (CJN), Olukayode Ariwoola, ya gargadi sabbin alƙalan babbar kotun tarayya da su kauracewa karbar cin hanci da rashawa.
Ariwoola ya ce sau da dama ana sukar alkalan Najeriya bayan sun yanke hukunci saboda zargin ana basu na goro, don haka ya nuna muhimmancin amfani da doka zalla a shari'a.
Asali: Legit.ng