Zasu sha jar miya: Matsayi da sabon albashin alkalan Najeriya bayan hukuncin NIC

Zasu sha jar miya: Matsayi da sabon albashin alkalan Najeriya bayan hukuncin NIC

  • Sabuwar dokar kotun masana'antu ta Najeriya ta ceto alkalan Najeriya inda aka ninnika musu albashinsu daga wanda suke karba a baya
  • A baya, CJN yana karban N3 miliyan ne a wata amma yanzu ya koma N10 miliyan kamar yadda mai sharia Obaseki-Osaghae ta yanke
  • Obaseki-Osaghae ta yanke hukuncin ranar Juma'a, 15 ga watan Yuli inda tace kin gyara albashin na shekaru 24 rashin adalci ne

FCT, Abuja - Tun bayan da aka gyara albashin ma'aikatan shari'a a 2008, an tilasta gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sake duba tare da kara albashin ma'aikatan shari'a na kasar nan.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sabon cigaban ya tabbata ne yayin da kotun masana'antu ta Najeriya ta bada umarnin a ranar Juma'a, 15 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

Olukayode Ariwoola
Matakin alkalan Najeriya da sabon albashin da zasu dinga karba bayan hukuncin NIC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, Mai shari'a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae wacce ta yanke hukuncin ta kwatanta gazawar gwamnati na kara albashin kafin nan da rashin adalci da kuma kin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar nan.

Hukuncinta ya kawo sabon tsarin albashi na ma'aikatan shari'a mataki zuwa mataki.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ga sabon albashin yadda yake:

1. Alkalin alkalan Najeriya zai dinga karbar N10 miliyan a wata.

2. Alkalan kotun koli zasu dinga karbar N9 miliyan a wata.

3. Shugaban kotun daukaka kara zai dinga karbar N9 miliyan a wata

4. Alkalan kotun daukaka kara zasu dinga karbar N8 miliyan a wata.

5. Manyan alkalan kotun tarayya zasu dinga karbar N7 miliyan a wata.

6. Manyan alkalan kotun jiha zasu dinga karbar N7 miliyan a wata.

7. Babban alkalin FCT zai dinga karbar N7 miliyan a wata.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

8. Kotun daukaka kara ta shari'a - N7 miliyan a wata.

9. Shugaban kotun daukaka kara ta gargajiya na FCT zai dinga karbar N7 miliyan a wata.

A nan bangaren, Daily Nigerian ta rahoto cewa, masu shari'a da alkalai a yanzu haka suna karbar N3 miliyan da kasa da hakan a matsayin albashi.

CJN Tanko Yayi wa Alkalai Martani Bayan Sun Zargesa da Shan Jar Miya Shi Kadai

A wani labari na daban, Shugaban alkalan Najeriya, Ibrahim Muhammad, ya yi martani ga alkalan da suka zargesa da rashawa.

Daily Trust ta ruwaito yadda alkalai 14 suka tura wa Muhammad wasika, wanda suka yi ikirarin ya dauki tsawon lokaci yana tauye musu hakkinsu.

Alkalan sun ce horarwan da ake musu na lamurran waje duk bayan shekara, ana yi ne don inganta alkalancin kasar, sai dai Muhammad ya toshe wannan kafar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel