Hotuna: Fasto ya ba 'yan matan coci satifiket din budurci bayan yi musu gwaji da tantancewa

Hotuna: Fasto ya ba 'yan matan coci satifiket din budurci bayan yi musu gwaji da tantancewa

  • Nazareth Baptist Church ta yi wa 'yan matan cocin da suka wuce shekaru 18 gwajin budurci kuma ta ba wadanda suka tsallake gwajin satifiket
  • An gano cewa, ana yi wannan gwajin duk shekarar ne ga 'yan matan kuma a yi musu alamar tsarki a goshi har zuwa shekara mai zuwa da za a yi sabon gwaji
  • Satifiket din budurcin yana samun sa hannun shugaban cocin da kuma kwararren da yake tantance budurcin 'yan mata

Wata coci a kasar Afrika ta kudu ta yi wa 'yan matan cocin gwaji da tantancewa kan budurcinsu kuma ta bai wa kowacce budurwa satifiket matukar ta tsallake.

An kirkiro wannan gwajin ne a kokarin cocin na kara kwarin guiwar kame kai daga badala a al'umma.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta nemi gwamnati ta mata bayani akan yadda ake kashe kudin tsaro

Budurci
Hotuna: Fasto ya ba 'yan matan coci satifiket din budurci bayan yi musu gwaji da tantancewa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Budurci
Hotuna: Fasto ya ba 'yan matan coci satifiket din budurci bayan yi musu gwaji da tantancewa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurci
Hotuna: Fasto ya ba 'yan matan coci satifiket din budurci bayan yi musu gwaji da tantancewa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Cocin mai suna Nazaretjh Baptist Church tana nan a Ebuhleni, arewacin Durban dake kasar Afrika ta kudu.

An tattaro yadda cocin ta yi gwajin budurcin ga 'yan mata masu halartar cocin kyauta kuma wadanda suka wuce shekaru 18, LIB ta ruwaito.

Wannan gwajin duk shekara cocin take yi, kuma bayan an kammala sai a bada satifiket din budurci ga wadanda suka yi nasarar tsallakewa.

Hakazalika, ana yin wata alama ga matan ta hanyar manna musu farin abu a goshi wanda ake kira da alamar tsarki, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ana yin gwajin ne a tsakiyar kowacce shekara kuma satifiket din na amfani daga rabi na karshen shekarar har zuwa rabin sabuwar shekara lokacin da za a sake yin gwajin budurcin.

Gwajin budurcin shekarar 2022/2023 an yi shi ne a makon nan kuma an bai wa 'yan matan da suka tsallake satifiket dinsu a hannu.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Satifiket din ya samu sa hannun shugaban Nazareth Baptist Church da kuma kwararren da yayi musu gwajin.

Hotunan da aka wallafa a yanar gizo sun bayyana yadda 'yan matan da aka tabbatar da budurcinsu suka cika da murna kuma suke ta daukan hotuna da satifiket dinsu.

Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin

A wani labari na daban, ko kana tunanin ka gama ji da ganin abun al'ajabi? To ga labarin wani Sarki a Mexico da ya auri Kada wanda zai daure maka kai.

Rahotanni sun bayyana yadda Sarkin, Victor Hugo Sosa na kauyen Pedro Humelula ya auri kada da ke sanye da rigar aure tare da kulla alakar aure ta hanyar sumbatarta cike da soyayya.

An gano yadda shagalin bikin ya kasance wani bangare na al'ada don kawo yalwa ga kauyen kudu maso yammacin Mexico.

Asali: Legit.ng

Online view pixel