Ana Cikin Jimamin Kisan Sojoji a Delta, Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki da Hafsoshin Tsaro
- Hafsoshin tsaro sun amsa gayyatar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zuwa fadarsa da ke Aso Rock Villa a Abuja
- Shugaban ƙasar ya yi buɗa baki tare da hafsoshin tsaron ne a sabon babban ɗakin taro na Banquet Hall da ke cikin fadar shugaban ƙasa
- Mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da shugabannin ma'aikatu da hukumomi na daga cikin waɗanda aka yi buɗa bakin tare da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin hafsoshin tsaron domin buɗa bakin azumin watan Ramadan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ɓuɗa bakin na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kace-nace kan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Delta a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.
Su wa Tinubu ya yi buɗa baki da su?
Shugaban ƙasan ya kuma karɓi baƙuncin mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), shugabannin ma’aikatu da hukumomi, a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Maris, domin buɗa baki a watan Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin majalisar ministoci da dama sun taru a cikin sabon ɗakin taro na Banquet dake fadar shugaban ƙasa domin buɗa baki tare da Shugaba Tinubu, cewar rahoton jaridar The Nation.
A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, shugaban kasar ya karɓi baƙuncin gwamnonin 36 na ƙasar nan, jim kaɗan bayan kashe sojoji 16 a yankin Okuama dake jihar Delta.
Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe Kwamanda ɗaya, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12 bayan sun yi musu kwanton ɓauna.
Shugaba Tinubu ya gana da Oberevwori
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oberovwori a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.
Gwamnan ya ziyarci shugaban ƙasan kan ta'adin da aka yi na halaka sojoji 16 a yankin Okuama na ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar.
Gwamnan a yayin ziyarar ya yi wa shugaban ƙasan cikakken bayani kan yadda lamarin mara daɗi ya auku.
Asali: Legit.ng