DHQ Ta Fitar da Cikakken Jerin Sunaye da Hotunan Dakarun Sojojin da Aka Kashe a Jihar PDP

DHQ Ta Fitar da Cikakken Jerin Sunaye da Hotunan Dakarun Sojojin da Aka Kashe a Jihar PDP

  • Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta yi alhinin dakarun rundunar sojojin da aka kashe a kauyen Okuama a jihar Delta
  • DHQ ta fitar da sunaye da hotunan sojojin da suka mutu a mummunan lamarin ranar Litinin, 18 ga watan Maria, 2024 a shafinta na X
  • A cewar hedkwatar tsaron, laftanar kanal, manjoji guda biyu da dakarun sojoji 13 ne suka rasa rayukansu a yankin ƙaramar hukumar Ughelli

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya da ke birnin tarayya Abuja ta wallafa sunaye da hotunan jami'an rundunar sojojin da aka kashe a ƙauyen Okuama, karamar hukumae Ughelli ta jihar Delta.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da DHQ ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 18 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Mataki mai karfi da hukumar soji ta dauka a Delta bayan kashe mata jami'ai 16

Sojojin Najeriya.
DHQ Ta Bayyana Sunaye da Hotuna Dakarun Sojojin da Aka Kashe a Jihar Delta Hoto: @DHQNigerianArmy
Asali: Twitter

A cewar DHQ, jami'an sojoji 17 aka kashe ciki har da laftanar kanal, manjoji da kyaftin na rundunar sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hedkwatar tsaron ta yi addu'ar Allah ya jiƙan gwarazan sojojin da suka rasa rayuwarsu a wannan mummunan lamari da ya afku a jihar Delta.

Ƴan Najeriya sun mayar da martani

@ontimesam ya ce:

"Wannan labarin naku bai ba kwata-kwata, me manjo guda biyu da laftanar kanal suke yi wurin? Ina tunanin kuɗin mai ko fashin filaye ya kai su."

@phychem11 ya ce:

"Wai ta ya matasa zauna gari banza zasu iya kashe sojoji masu cikakken horo haka a ɓagas ba tare sun masu illa ba? Gaba ɗaya wannan lamarin yana da ban mamaki.
"Ina miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansu."

@DrofComputing ya mayar da martani da cewa:

"Ina rokon Allah ya bai wa danginsu karfin guiwar jure wannan rashi."

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

@RealQueenBee__ ta ce:

"Allah ya ji kansu. Rundunar soji ta ce sun je aikin wanzar da zaman lafiya ne a Okuama, shin yaƙi ne ya ɓarke a kauyen da ake buƙatar zaman lafiya kamar dai abin da ya faru a Mogadishu.
"Yaushe sojoji suka koma masu samar da zaman lafiya? Yaushe rundunar soji ta zama kotu ko na ce ƴan sanda da har za ta riƙa shiga tsakanin abin da ya shafi fararen hula.
"Sojoji su fito su bayyana abin da ya kaisu Okuama da har suka tafi da laftanar kanal, manjo janar guda uku da wasu jami'an sojoji."

Bankin CBN ya fara korar daraktoci

A wani rahoton kuma Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara shirin korar daraktoci 19 daga aiki bayan matakin da ya ɗauka ranar Jumu'a da ta gabata.

Rahoto ya nuna CBN ya kori daraktoci bakwai a makon jiya, biyar daga cikin sun lashi takobin neman adalci a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262