Gidauniyar Dangote ta ware $50m domin magance karancin abinci a Najeriya

Gidauniyar Dangote ta ware $50m domin magance karancin abinci a Najeriya

Mun samu cewa Dangote Foundation, gidauniyar hamshakin attijiran nan Alhaji Aliko Dangote, ta ware zunzurutun dukiya ta Dalar Amurka miliyan 50 domin magance yunwa da kuma cututtuka masu nasaba da karancin abinci masu gina jiki a fadin Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito, gidauniyar bisa jagorancin shugaban ta, Aliko, ta daura kudiri aniyya tare da daura damarar tattalin abinci masu gina jiki domin magance cuttuka masu nasaba da yunwa musamman a tsakankanin yara.

Yayin bayyana hakan cikin jihar Legas a jiya Laraba, shugaban gidauniyar reshen kula da harkokin lafiya, Francis Aminu, ya bayyana cewa samar da ingatattun abincin masu gina jiki ya na da muhimmancin gaske wajen gina wani ginshiki na makoma mai kyau ga kasar nan.

Gidauniyar Dangote ta ware $50m domin magance karancin abinci a Najeriya
Gidauniyar Dangote ta ware $50m domin magance karancin abinci a Najeriya
Asali: UGC

A nasa jawaban, shugaban cibiyar Harvest Plus Nigeria, Paul Ilona, ya bayyana cewa nakasun abincin masu gina na da tasirin gaske kan al'ummar kasar nan da illarsa a halin yanzu ke kawo zagon kasa ga tattalin arzikin kasa.

KARANTA KUMA: 2019: Ba bu tasirin da Taron Dangi zai yi akan Buhari - Femi Adesina

Ya kara da cewa, Najeriya ta na asarar kimanin N450b a kowace shekara a sanadiyar karanci da nakasun sunadarai masu gina lafiyar jikin dan Adam musamman na Vitamins da Minerals.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata tsohuwar Gada da ta shekara 51 ta rushe yayin saukar ruwan sama mai tsananin gaske a jihar Taraba.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel