An Samu Asarar Rayuka Bayan Fusatattun Sojoji Sun Kona Gidaje a Bayelsa
- Dakarun sojoji sun kai farmaki a ƙauƴen Igbomotoru da ke jihar Bayelsa bayan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Delta
- Jami'an tsaron sun ƙona gidaje uku wanda ake zargin maɓoyar shugaban ƴan ta'addan da suka aikata aika-aikar ne
- A yayin farmakin aƙalla mutum 11 suka rasu, yayin da mazauna ƙauyen suka nemi da a kawo musu agajin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Biyo bayan kashe sojoji 16 a ƙauyen Okuoma da ke jihar Delta, dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki a ƙauyen Igbomotoru da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa.
A yayin farmakin sojojin sun lalata gidaje tare da kashe kimanin aƙalla mutum 11.
Meyasa sojoji suka farmaki ƙauyen?
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sojojin sun je ƙauyen ne cikin kwale-kwale guda biyar inda suka ƙona gidaje uku da ake zargin na wani shugaban ƴan ta'addan da ke da hannu a kisan da aka yi wa sojoji a Delta ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana cewa sojojin na dira ƙauyen, suka buɗe wuta kan wasu mutane da ke hutawa a bakin ruwa, daga bisani suka wuce suka ƙona gidaje ukun da ake zargin maɓuyar shugaban ƴan ta'addan ne.
Ya bayyana cewa mutanen ƙauyen sun dauko gawawwaki 11 daga harin, yayin da suke ci gaba da neman sauran.
A kalamansa:
"Farmakin sojojin ya taɓa rayuwar mutane sosai. Rayuka da dama sun salwanta, an yi asarar dukiyoyi. Ko bayan harin, na tabbata cewa rayuwa a ƙauyen ba za ta taɓa dawowa kamar da ba.
"Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su gaggauta shiga tsakani kan lamarin nan. Ba mu da hannu a abin da ya faru a jihar Delta. Ya kamata ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su kawo mana agaji."
Me sojoji suka ce kan lamarin?
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin 'Operation Delta Safe' (OPDS), Manjo Adenegan Ojo, kan lamarin sai ya yanke kiran bayan ya fahimci ɗan jarida ne.
Daga nan kuma bai sake ɗaukar kiraye-kirayen da aka yi masa ta wayar salula ba.
Kisan sojoji 16: Tinubu ya yi martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi martani kan kisan sojoji 16 da aka yi a wani kauye da ke jihar Delta.
Shugaba Tinubu ya ba babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa umarnin zaƙulo waɗanda ke da hannu a kisan don fuskantar hukunci.
Asali: Legit.ng