Yan Majalisa 8 da Aka Dakatar a Jihar Arewa Sun Yi Zargin ‘Ana Barazanar Kashe Su’

Yan Majalisa 8 da Aka Dakatar a Jihar Arewa Sun Yi Zargin ‘Ana Barazanar Kashe Su’

  • Wasu 'yan majalisa takwas da aka dakatar da su a jihar Zamfara, sun yi ikirarin cewa 'yan daba na farautar rayuwarsu domin su halaka su
  • A cewar 'yan majalisar, sun yi gudun hijira daga Zamfara saboda su tsira da rayukansu, kuma an nemi su mayar da motocin da aka ba su
  • 'Yan majalisar, sun yi ikirarin cewa an dakatar da su ne saboda sun fadi gaskiya game da yadda matsalar tsaro ta ta'azzara a mahaifarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara - 'Yan majalisa takwas da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da su sun ce 'yan daba na farautar rayuwarsu saboda sun fallasa ta'azzarar tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Yahaya Bello na fuskantar sabuwar matsala, EFCC ta sake kai shi kotu

A yayin da suka sanar da hakan a ranar Lahadi, 'yan majalisar sun bayyana cewa yanzu haka sun yi gudun hijira daga jihar kuma an nemi su mayar da motocin da aka ba su.

Majalisar dokokin jihar Zamfara
'Yan majalisar da aka dakatar a Zamfara sun yi zargin ana farautar rayuwarsu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a ranar 27 ga watan Fabrairu, majalisar Zamfara ta dakatar da 'yan majalisar takwas saboda zargin sun yi wani haramtaccen zaman majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisar Zamfara 8 da aka dakatar

'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da; Bashir Aliyu (PDP-Gummi 1); Amiru Keta (PDP-Tsafe ta Yamma); Nasiru Abdullahi (PDP-Maru ta Kudu) da Bashir Masama (PDP-Bukkuyum ta Arewa).

Sauran sun hada da; Faruku Dosara (APC-Maradun 1); Ibrahim Tukur (APC-Bakura); Shamsudeen Hassan (APC Talata-Mafara ta Arewa) da Bashiru Sarkin-Zango (PDP-Bungudu ta Yamma).

Da suke zanta wa da manema labarai a Zariya, jihar Kaduna, Jaridar Leadership ta rahoto 'yan majalisar sun yi ikirarin cewa an tura wasu 'yan bangar siyasa domin su farauci rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Buga takardun bogi: Kotu ta dauki mataki kan tsohon shugaban bankin NIRSAL, Abdulhameed

Yadda 'yan daba ke bibiyar 'yan majalisa

Bashir Aliyu, wanda ya yi magana a madadin 'yan majalisar da aka dakatar, ya ce wannan barazanar ba za ta hana su yin magana kan matsalolin tsaro a Zamfara ba.

Ya ce sun yi yunkurin kawo sauyi a shugabancin majalisar jihar ne domin ankarar da mutane kan tsawon lokacin da ka dauka ba tare da ganin kakakin majalisa da mataimakinsa ba a zauren majalisar ba.

Sai dai, ya ce tun a wannan lokaci ne wasu 'yan daba ke bibiyar rayuwarsu domin halaka su maimakon su hada kai domin kawo zaman lafiya a jihar.

"Ana yi wa dimokuraɗiyya barazana" - Aliyu

Rahoton The Guardian ya nuna cewa Aliyu ya yi ikirarin an kai wa wasu daga korarrun 'yan majalisar farmaki a taron bikin diyar mataimakin gwamnan jihar a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Aliyu, wanda ke wakiltar mazabar Gumi 1, ya ce:

Kara karanta wannan

Ningi: Jerin sanatocin Najeriya da aka dakatar daga 1999 zuwa 2024 da kuma dalilin da ya sa

"Muna so mu sanar da ku cewa akwai tarin matsalolin tsaro da ke addabar jihar Zamfara, amma maimakon kawo karshen hakan, an ɓuge da yi wa dimokuraɗiyya barazana."

Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki kauyen Nasarawa Godel, inda suka kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu 20.

Kauyen Nasarawa Godel na cikin karamar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara, kuma sun dade suna fama da hare-haren 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.