Jami'an Tsaro Sun Hallaka Kasurgumin Shugaban 'Yan Bindiga a Jihar Arewa
- An rage mugun iri a jihar Katsina bayan jami'an tsaro na ƴan sa-kai sun samu nasarar sheƙe ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar
- Ƴan sa-kan tare da jami'an tsaro sun sheƙe Kachalla Maude ne bayan sun yi masa kwanton-ɓauna a ƙaramar hukumar Batsari
- Kachalla ya daɗe yana kai hare-hare kan bayin Allah, inda kafin a kashe shi ya amsa cewa ya karɓi kuɗin fansa fiye da N130m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan sa-kai sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Kachalla Maude, a jihar Katsina.
Ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Katsina ta tabbatar da samun wannan nasarar ta sheƙe shugaban ƴan bindigan, wanda ya addabi al'ummar jihar, cewar rahoton gidan talabijin na Channels tv.
Yadda aka kashe Kachalla Maude
Jami'an ƴan sa-kan tare da goyon bayan jami'an tsaro sun yi wa tawagar mayaƙan Kachalla Maude, kwanton ɓauna ne a ƙauyen Garin Rinji da ke yammacin ƙaramar hukumar Batsari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar Katsina, Bala Zango, ya fitar a ranar Lahadi, ta tabbatar da kawo ƙarshen numfashin Kachalla Maude a duniya, rahoton da jaridar Leadership ya tabbatar.
Ya bayyana cewa a yayin harin kwanton ɓaunan da ƴan sa-kan suka yi wa ƴan ta’addan, sun yi musu ruwan wuta wanda ya kai ga cafke shugabansu.
Ya ce Maude da ƙungiyarsa sun addabi yankin yammacin ƙaramar hukumar Batsari da ke jihar.
Kachalla Maude ya daɗe yana kai hare-hare
Kwamishinan ya ce kafin a tura Maude zuwa lahira, ya yi iƙirarin cewa shi ne ya jagoranci hare-haren da aka kai kan ƙauyuka da dama da ke kan hanyar Batsari/Danmusa.
Hare-haren dai sun yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya kuma amsa laifin karɓar sama da N130m daga iyalan mutanen da ya yi garkuwa da su a matsayin kuɗin fansa.
Ƴan ta'adda sun kai hari a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan ta'adɗa sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Ƴan ta'addan waɗanda suka farmaki ƙauyen Dogon-Noma sun salwantar da rayukan mutane masu yawa a yayin harin.
Asali: Legit.ng