Dan Najeriya Ya Girgiza Intanet Ta Hanyar Daga Buhun Shinkafa da Hakoransa
- Wani bidiyo mai daukar hankali na wani mutum mai motsa jiki dan Najeriya yana daga buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 da hakoransa ya dauki hankulan mutane a yanar gizo
- Faifan bidiyo ya nuna mutumin da karfin gwiwa ya tunkari buhun shinkafar kafin daga bisani ya sa bakinsa ya raba shi da kasa
- Yadda ya dauki buhun da kuma yadda ya daidaita shi a iska ne ya bar 'yan kallo a kafar sada zumunta cikin matukar mamaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Wani bidiyon mai daukar hankali na wani malamin motsa jiki ya ba da mamaki a lokacin da aka ga yana daga buhun shinkafa mai daukin kiligiram 50 da hakoransa.
Bidiyon ya nuna karfi da kuzarin mutumin, inda aka ga ya tunkari buhun cikin sauki tare da raba shi da kasa zuwa kusa da bakinsa.
Masu kallo dai an bar su cikin mamaki, inda suke ta'ajibin yadda ya iya daukar abu mai nauyi da bakinsa ba tare da wata matsala ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da jama'a ke cewa bayan ganin ya daga buhu da hakora
Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke yabawa da irin karfinsa wasu kuma ke mamakin yadda jikinsa ya iya jure nauyin.
Wannan gwada kwanji da karfi ya tura sako mai karfi ga mutanen duniya. Masu kallo daga kasashen duniya sun bayyana ra'ayoyinsu masu daukar hankali.
Sai dai, wasu basu gamsu da hakan ba, inda suka bayyana rashin yarda da aukuwar lamari irin wannan, a cewarsu hakan bai kama hankali ba.
Duk da haka, wannan bidiyo ya nuna irin tasirin karfin da Allah ke yiwa wasu daga cikin mutane da kuma ba su kuzari marar misaltuwa.
Kalli bidiyon a kasa:
Motsa jiki ga jikin danadam
A baya mun kawo muku rahotanni kan wasu abubuwan da ka iya zama sanadin dawwamar lafiyar jiki ga danadam.
Akwai hanyoyin motsa jiki da idan mutum ya maida hankali a kansu, to babu bukatar sai ya je asibiti dubiya.
Hakazalika, an ce irin wannan motsa jiki ka iya jawo karfin basira da kaifin gani duba da fa'idarsa a jikin danadam.
Asali: Legit.ng