Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya

Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya

- Ya kawo ziyara kasashen Afirka, inda ya gana da shuwagabanni

- Yace 'Naija no dey carry last'

- Shi ake sa rai zai gaji Sarauniya Izzabul in ta rasu a Ingila

Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya
Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya
Asali: UGC

Shekara da shekaru, yakin yaqi karewa, tsakanin kasashen Afirka, kan wai wa ya iya dafa shinkafa jollof, inda kowa ke ganin shi ke kan gaba a nahiyar, inda a bara kuma yakin ya barke tsakanin Najeriya da Ghana.

Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya
Yakin Jollof Rice: Yariman Ingila ya shiga tsakanin yakin cacar baka da ake yi tsakanin Ghana da Najeriya
Asali: Twitter

An shafe makonni, aka kuma shiga watanni a shafukan labarai, musamman na sada zumunta, inda ake gwada kwanji kan wa ya iya waye bai iya ba.

Jama'a daga kasashe dai, sunyi amanna Najeriya na kan gaba wajen iya girki na gargajiya, musamman yadda ake zuwa Restaurant na Najeriya a wadannan kasashe kamar a ci da gashi.

DUBA WANNAN: Boko Haram na kokarin dawowa barazana

Yanzu dai fadan yazo karshe, bayan da mai jiran gadon sarautar Ingila ya sanya baki, ya kuma tabbbatar wa duniya da cewa, ba makawa, Najeriya bata daukar na karshe a duniya, inda ya fadi da broken Ingilishi; Naija no dey carry last!

Watau dai a cewarsa, bayan ya dandana dukkan abincin na kasashen biyu, a ziyarar sa ta makon jiya, ya tabbatar wa kansa wa yafi iya girki da zabga kayan qamshi, amma yace ba zai iya fadi a ili ba, saboda kada ya qara rura wutar yakin, don haka zai ja bakinsa yayi tsit.

An sha raha dai da wadannan kalamai nasa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel