In dai kuna yin wadannan abubuwan, to ba sai kaje asibiti ganin likita ba

In dai kuna yin wadannan abubuwan, to ba sai kaje asibiti ganin likita ba

- Hanyar samun lafiya kyauta ba tare da an biya kowa ko sisi ba

- Da mutane zasu gane, su rika binta kullum da sun ragewa likotoci cunkoso a asibiti

Shin ko kasan yadda yin tafiya yake mutukar taimakawa jikin dan Adam kuwa? Tabbas idan ka karanta wannan bayani ba zaka daina tafiyar kafa a kullum ba domin cigaba da samun alfanunta.

Kai bari kuji mai gaba daya wai haihuwa da hanji, da mutum zai hada tafiyar kafa kamar ta mintuna goma sha biyar zuwa talatin a rana, da cin lafiyayen abinci mai gina jiki tare da samun isasshen bacci, to da ya hutu da zuwa wurin likita akai-akai da sunan rashin lafiya.

Yin wannan tafiya a matsayin motsa jiki, na mutukar taimakawa wurin habaka lafiyar ganganjikin dan Adam.

Legit.ng tayi muku nazarin wadannan abubuwan da zasu baku mamaki akan cewa zaku daina zuwa asibiti akai-akai da sunan rashin lafiya.

Wani abin dadi ma shi ne, tafiyar kafar kyauta ce babu kudin da zaku biya balle wani yace tayi masa tsada.

Karanta kuji, irin alfanun da zaku samu mutukar kuka juri tafiyar kafar a matsayin hanyar motsa jiki don samun lafiya.

1. Karin kaifin basira

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Kwakwalwar Mutum

Bincike ya nuna cewa, motsa jiki kamar tafiyar kafa na taimakawa wajen iza wutar kaifin basira tare da dakile dusashewar kwakwalwa wadda ke haddasa lalular dolanci. Sannan kuma tafiyar kafar na taimakawa warin rage yawan gajiyar kwakwalwa.

2. Kara karfin gani

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Idon Mutum

Duk wanda ba shi da ido to tabbas yayi mutuwar tsaye, to amma shin menene ala’kar tafiyar kafa da ido?

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Farfesa Sagay

Tafiyar kafa na da tasiri sosai wajen taimakawa ido, halasi ma tafiyar kafar na yakar mummunar cutar dusashewar gani da ke kashe ido (Glaucoma).

3. Kariya daga ciwon zuciya

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Zuciyar Mutum

A bisa binciken da kungiyar kula da lafiyar zuciya ta kasa Amurka ta yi, ya nuna cewa, yin gudu a matsayin motsa jiki bai fi yin tafiya kafa bayar da gudunmawa ga lafiyar zuciya ba. Wannan hanya dai na taimakawa waje rage hauhawar jinni gami da kona kitsen da yake wahalar narkewa wato (cholesterol), tare da saukaka gudanar zagayawar jini a cikin jiki..

4. Gyaran bututun numfashi

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Hunhun Mutum

Yin tafiyar kafa na taimakawa hunhu samun damar shaka da fitar da wadatacciyar iska, da kuma ba shi damar fitar da dattin da ke makalewa a sassan hunhun sakamakon aiki da sauri da yake yi idan kayi gudu ko tafiya.

5. Daidaita Sigan da jiki ke bukata

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Masarrafar jikin Mutum

Binciken da aka gudanar akan wasu masu ciwon siga ya nuna cewa adadin sigan jikinsu ya saisaita da kimanin kashi shida (6%), bayan fara tafiya da suka yi a matsayin hanyar neman lafiya. Asaboda haka idan kuna burin samun daidaiton adadin sigan jiki, ga hanya mai sauka.

6. Taimakawa waje narkar da abincin

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Hanjin Mutum

Ko tantama babu tafiya na taimakawa waje narkar da abincin da aka ci, don kimanin fiye da shekaruko dubu biyu aka fada a cikin wani Hadisi. Don haka domin samun karin lafiya, idan anci abinci kada a zauna balle a kwanta, don hakan na haifar da cushewar ciki da magwas (gyatsa mai wari) ko kuma ya janyo gyambun ciki.

7. Rage nauyin tare da gyran jiki

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba

Idan akwai hanya mai sauki da mutum zai iya rage teba idan tayi masa yawa ko kuma yana son yin kwanji, to gudu ne yafi dacewa da shi.

8. Saita gabobi

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Gwuiwa

Gabobin mutane na bukatar motsa jiki, kuma tafiyar kafa ka iya wadatar da hakan,tare da rage hadarin saurin karaya. A dalilin haka ne cibiyar Arthritis Foundation tayi kira da cewa yana da kyau a kalla mutum yayi tafiyar mintuna 30 a kullum, domin hakan zai rage duk wani zafi ko ciwo da gaba ke ji..

9. Magance matsalar ciwon baya

In dai kana yin wadannan abubuwan to ba sai kaje asibiti ganin likita ba
Ciwon baya

Lallai tafiyar kafa hanya ce da zata ceci rayuwar mutane da dama domin kuwa ga duk mai fama da matsalar ciwon bayan da ya takura masa, to ga hanya sahihiya mai sauki ta yin tafiyar kafa a kullum, kamar ta mintuna 15 - 30. kamar yadda brightside.me suka wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng