Rayuwa Ba Tabbas: Direba Ya Fadi Ya Rasu Yana Tsaka da Tuka Dalibai Zuwa Makaranta

Rayuwa Ba Tabbas: Direba Ya Fadi Ya Rasu Yana Tsaka da Tuka Dalibai Zuwa Makaranta

  • Mahukuntan jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara sun shiga cikin damuwa sakamakon mutuwar wani direba
  • Direban, yayin da yake kai wasu ɗalibai zuwa harabar jami’ar, ya rasa ransa bayan kwatsam ya yanke jiki ya faɗi
  • Daraktan yaɗa labarai na jami’ar Ilorin, Mista Kunle Akogun, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara - Wani direban motar bas mai suna Lukman ya rasa ransa yayin da yake kai wasu ɗalibai harabar jami’ar Ilọrin (UNILORIN) da ke jihar Kwara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, wannan mummunan lamarin da ya faru a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, ya bar mutanen da ke cikin motar cikin firgici.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Direba ya rasu a jami'ar Ilorin
An shiga jimamin rasuwar direban mota a jami'ar Ilorin Hoto: UNILORIN
Asali: Facebook

Wani fasinja da lamarin ya faru a gaban idonsa ya bayyana cewa shi ya ya ci gaba da tuƙa motar bas ɗin a wani yunƙuri na ceto sauran ɗalibai da kuma kaucewa aukuwar bala’i, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

A kalamansa:

"Direban bas ɗinmu ya mutu ne a kan hanya yayin da yake tuƙa mu daga Sanrab zuwa Unilorin. Ina zaune a gaba amma ban lura ba saboda ina karatun Alkur’ani a wayata."

Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin, Sulyman Malik, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin tattaunawa ta wayar tarho.

Ya bayyana cewa direban ya yi masa jaje ranar Alhamis, 14 ga watan Maris game da wani hatsarin da ya auku da shi a baya-bayan nan.

A kalamansa:

"Daga abin da muka tattara, ya gama haye ƙabarin mai tatsine na huɗu da ke a kwanar bayan kofar makaranta, yana tafiya zuwa wurin ajiye motoci lokacin da ya faɗi."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

Da yake mayar da martani, daraktan yaɗa labarai na jami’ar Ilorin, Mista Kunle Akogun, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma tunatar da rashin tabbas na rayuwa.

Ɗaliba ta halaka kanta a Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ɗalibar ƴar aji huɗu a jami'ar jihar Kwara ta yanke shawarar barin duniya.

Ɗalibar mai suna Rashidat Shittu ta ɗauki ranta ne bayan ta ci karo da matsala a karatun da take yi a jami'ar wacce ke a ƙaramar hukumar Moro ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng