Sace-Sace a Kaduna da Borno: An Ba Shugaba Tinubu Mafita

Sace-Sace a Kaduna da Borno: An Ba Shugaba Tinubu Mafita

  • Wasu ƙungiyoyin ƴan Najeriya sun shaidawa Shugaba Bola Tinubu cewa ya bi hanyar tattaunawa don kuɓutar da ɗalibai 287 da malamansu da aka sace a Kaduna
  • Gidauniyar Kalthum Foundation for Peace (KFP) ta yi wannan kiran ga shugaban ƙasan a Abuja a ranar Juma’a 15 ga watan Maris
  • Sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta zauna da ƴan bindigan ta gano koke-kokensu da matsalolinsu domin a shawo kan matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki salon tattaunawa wajen ceto ɗalibai da matan da aka sace a jihohin Kaduna da Borno.

Gidauniyar Kalthum Foundation for Peace (KFP) ta yi wannan roko a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, a wani taron manema labarai a Abuja wanda Legit.ng ta halarta.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

An bukaci Tinubu ya yi sulhu da 'yan bindiga
Gidauniyar Khalthum ta bukaci Tinubu ya yi sulhu da 'yan bindiga Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Idan dai za a iya tunawa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari Kuriga, inda suka yi awon gaba da ɗalibai kusam 287.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mummunan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da ƴan ta'adda sun sace mata ƴan gudun hijira sama da 200 a jihar Borno.

Da take zantawa da Legit.ng, shugaban gidauniyar, Amb. Ummu Kalthum Muhammad ta ce dole ne a bi hanyar yin sulhu.

A kalamanta:

"Ƴaƴan talakawa ne ake sacewa, kamar yadda na fada a jihar Borno, ƴan gudun hijira ne aka sace, don haka idan yau wasu mutane ne da ƴaransu, gobe ƴaƴanmu ne za a sace.
"Don haka ya zama dole mu goyi bayan iyalan waɗannan mutane domin ganin cewa idan har sulhu da tattaunawa da su ita ce hanyar da ta dace, to ya kamata a yi hakan."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi kuskuren da gwamnati ke yi wajen ceto daliban da aka sace a Kaduna

An buƙaci FG ta saurari ƙorafe-ƙorafen ƴan bindiga

Shi ma da yake magana da Legit.ng, Dr Abubakar Sani, sakataren kwamitin amintattu na gidauniyar, yace dole ne gwamnatin tarayya ta bada damar tattaunawa.

Sai dai bai goyi bayan ra'ayin biyan kuɗin fansa ba, amma ya ba da shawarar cewa gwamnati ta gano matsalolin ƴan bindiga tare da cimma matsaya da su.

Dr Sani ya bayyana cewa:

"Ko muna so ko ba mu so, dole ne mu zauna da su. Wannan ita ce tattaunawa. Kuma Amurkawa sun yi da Taliban. Isra'ilawa suna yi da Falasɗinawa. Amma abin da nake ganin bai dace ba shi ne biyan kuɗin fansa.
"Amma idan tattaunawa ce a san menene ƙorafinsu, meyasa suke yin haka? Me suke so su cimmawa ta hanyar yin hakan? Ta iya yiwuwa suna so su ja hankalin gwamnati ne halin da yaransu suke ciki. Ba su samun ilmi, ba ingantaccen ruwan sha da sauransu."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

Gumi na son jagorantar sulhu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, na son jagorantar yin sulhu da ƴan bindigan da suka sace ɗalibai a Kaduna.

Sheikh ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da kada ya maimaita irin kuskuren da magabacinsa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng