Ana Cikin Azumi 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa

Ana Cikin Azumi 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa

  • Wasu miyagun ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
  • Sabon harin ta'addancin dai an kai shi ne a ƙauyen Dogon-Noma na ƙaramar hukumar da safiyar ranar Asabar, 16 ga watan Maris 2024
  • Harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun halaka mutum ɗaya tare da sace wasu mata takwas a ƙaramar hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - A safiyar yau Asabar ne ƴan ta’adda suka sake kai wani sabon hari a kan mutanan ƙauyen Dogon-noma da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Harin dai na zuwa ne kwanaki uku da kashe mutum ɗaya, tare da yin garkuwa da mata takwas a yankin Banono Angwaku na ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

'Yan ta'adda sun kai hari a Kaduna
Ana farbagar an halaka mutane a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya auku

Wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Cafra Caino, ya tabbatar wa jaridar The Punch aukuwar sabon harin a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 5:45 na safiyar ranar Asabar, inda suka zo da yawan gaske, yayin da suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi..

A kalamansa:

"Har yanzu ba mu sami adadin wadanda suka mutu ba saboda mutanen sun gudu don tsira da rayukansu a lokacin da maharan suka farmaki ƙauyen.
"A cikin shekarar 2019, mutanen ƙauyen sun fuskanci mummunan hari inda aka kashe mutum 74, kuma a kwanakin baya an riƙa kawo hare-hare a ƙauyen."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani kan aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fadi makudan kudin da za a biya kafin su sako daliban da suka sace a Kaduna

Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, kakakin rundunar bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.

Yaƙi da ƴan bindiga: Gumi ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya nuna kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen yaƙar ƴan bindiga.

Malamin ya bayyana cewa amfani da ƙarfi kan ƴan binɗigan ba zai haifar da ɗa mai ido ba wajen ganin an kawo ƙarshensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng