Ana Cikin Jimamin Sace Dalibai, Ƴan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Jihar Kaduna

Ana Cikin Jimamin Sace Dalibai, Ƴan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Jihar Kaduna

  • Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
  • A yayin harin da ɓata garin suka kai, sun salwantar da ran mutum ɗaya tare da yin awon gaba da mata bakwai da namiji ɗaya
  • Sun kuma kwashe dukiya mai tarin yawa da kayan abinci bayan sun riƙa bi gida-gida suna farmakar bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon hari a yankin Banono na ƙauyen Angwaku cikin masarautar Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A yayin harin, ƴan bindigan sun harbe wani mutum ɗaya har lahira, sannan suka yi awon gaba da wasu mutum takwas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Fasinjoji da dama sun bace yayin da 'yan bindiga suka farmaki wata mota a Taraba

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum takwas a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Kaduna

An bayyana sunan marigayin a matsayin Christopher Zamani. Wata mata kuma ta samu raunuka a yayin harin na ƴan bindigan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunayen mutanen da aka sacen sun haɗa da Tina Bulus, Alice Joshua, Sarah Micah, Kaduna Fidelis, Janet Amos, Martha Peter, Rita Geoffrey da Favor Ado.

Mary Isah, wacce ta samu raunuka a yayin harin, an kai ta asibitin Nasara Maternity Clinic da ke Marabar Kajuru domin duba lafiyarta.

A yayin harin dai ƴan bindigan sun kai farmaki gidajen mutane da dama tare da wawushe kayayyaki masu daraja da suka haɗa da kuɗi, kayan abinci da babura biyu.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nemi Naira tiriliyan 40 da abu 2 a matsayin kuɗin fansar mutane 16 a jihar Arewa

Sai dai har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.

Kaduna: Ƴan bindiga sun bindige masallata

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga kai hari kan masallata a Anguwar Makera ƙarƙashin garin Kwasakwasa na ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

A yayin harin da aka kai ana tsaka da sallar Juma'a, an hallaka mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel