Kotu ta daure karuwa wata 4 saboda gasawa kwastoma cizo a harshe

Kotu ta daure karuwa wata 4 saboda gasawa kwastoma cizo a harshe

  • Wata kotu a jihar Benue ta daure wata karuwa daurin watanni hudu a gidan yari ko sharar harabar kotu
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, karuwar ta ciji wani kwastomanta ne yayin da suke jima'i
  • A nata bangaren, ta ce ta cije shi ne saboda ya nemi karin lokaci a kan yadda suka yi ciniki da ita

Benue - Wata babbar Kotu a Makurdi a ranar Alhamis ta yanke hukuncin daurin wata hudu ga wata karuwa, Dooshima Anems, saboda cizon harshen kwastomanta yayin jima'i.

'Yan sanda sun tuhumi Anems da harar kwastomanta da kuma haddasa mummunan rauni a harshensa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai shari'a a kotun, Ms Rose Iyorshe, ta yankewa Anems hukunci bayan ta amsa laifin ta sannan ta shaidawa kotu cewa ta ciji Mista Amos Igbo ne don kare kanta.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

Kotu ta daure karuwa wata 4 saboda gasawa kwastoma cizo a harshe
Kotu ta daure karuwa bisa laifin cizon kwastoma | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Iyorshe a cikin hukuncinta ta ba Anems zabin tsaftace harabar kotun na mako guda.

Tun da farko, mai gabatar da kara na ‘yan sanda, Insp Veronica Shaagee ta shaida wa kotun cewa an cafke karuwar ne a ranar 28 ga watan Satumba.

Shaagee ta ce Anems ta ciji Mista Amos Igbo a harshen yayin jima'i a otal din Tekdee inda suka kwana.

Ta ce Igbo ya dauko Anems ne a Yaman Park ya kuma biya ta N2,000 a daren.

Ta ce laifin ya ci karo da sashi na 166 (b) da 248 na dokokin Penal Code Cap 124 (2004) na jihar Benue.

Tun da farko, Anems ta bayyana cewa Igbo na son karin lokaci da ita sabanin kudin da ya biya amma ta ki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

A cewarta:

”Ranki ya dade ya buge ni da karfi. Ni kuma na cije shi don kare kaina."

Gwamnati ta fara kidayar karuwai da ke zaune a jihar Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta fara wani aikin kidaya na mako daya domin sanin adadin karuwai da ke zaune a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan dindindin, Hukumar Hisban na jihar Bauchi, Aminu Balarabe, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da kidayar karuwan, a ranar Laraba a jihar Bauchi.

A cewar PM News, Balarabe ya ce an tsara shirin ne da niyar tallafawa karuwan da kudade don su dena karuwanci, su koyi sana'o'i su zama masu dogaro da kansu.

Ya ce gwamnatin jihar za ta taimakawa karuwan da ke son a sada su da yan uwansu, ya kara da cewa ba don cin mutuncinsu ko nuna wariya yasa aka bullo da shirin ba.

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

A cewarsa, kidayar, za ta taimakawa gwamnatin jihar ta yi shiri sosai ta kuma gano irin kudi da wasu abubuwan da ake bukata domin taimakawa karuwan su canja rayuwa

Wani mahaifi ya kashe dansa mai shekaru 2 da tsananin duka da bulala

A bangare guda, wani mutum mai suna Vwede ya lakadawa dansa mai shekaru biyu duka har lahira a Yenagoa, jihar Bayelsa kuma ya tsere, The Nation ta ruwaito.

Lamarin, wanda ya faru ranar Lahadi 26 ga watan Satumba a kan titin Imiringi a Yenagoa, ya jawo Allah wadai daga makwabta da masu rajin kare hakkin dan adam.

An tattaro cewa mahaifin da ake zargi, daga jihar Delta, ya yi wa yaron mai shekaru biyu bulala mai tsanani sannan ya kai shi asibiti a kan hanyar Ruthmore Hotel a Immiringi bayan yaron ya suma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel