Kashe $1.5bn don gyaran matatar man Fatakwal, da lauje cikin nadi: Cewar Atiku

Kashe $1.5bn don gyaran matatar man Fatakwal, da lauje cikin nadi: Cewar Atiku

- Gwamnatin Buhari na cigaba da shan suka kan yunkurin kashe kudi wajen gyaran matatar mai

- Yayinda wasu ke cewa a saurari Dangote ya kaddamar da nashi matatar

- Wasu sun ce kawai ana son amfani da kudi wajen yakin neman zaben 2023

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan jam'iyyar hamayya PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana ra'ayinsa kan makudan kudin da gwamnatin Buhari ke shirin kashewa wajen farfado da matatar man Fatakwal.

A ranar Laraba, karamin Ministan man Najeriya, Timipre Sylva, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sakin kudi $1.5bn don gyara matatar man Fatakwal.

Atiku ya ce ko sabon matatar mai ba za taci wannan kudin ba.

A cewarsa, babu hankali cikin kokarin kashe irin wadannan makudan kudi kan matatar man da babu riba cikinta a lokaci irin yanzu da ake cikin kakanikaye.

"A ce za'a kashe $1.5bn don gyara matatar man Fatakwal rashin tunani ke a wannan mumunan hali da muke ciki," Cewar Atiku.

"Bugu da kari. Wannan kudi ya yi yawa, ya wuce gona da iri saboda kamfanin Shell a bara ta sayar da matatar man Martinez dake California, Amurka, mai girma irin na Fatakwal a farashin $1.2bn."

"A sani cewa matatar man Shell Martinez ya fi amfani da riba fiye da matatar man Fatakwal."

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwa a kauyen Katsina, sun yi gaba da ‘ya ‘yansa

Kashe $1.5bn don gyaran matatar man Fatakwal, akwai lauje cikin nadi: Cewar Atiku
Kashe $1.5bn don gyaran matatar man Fatakwal, akwai lauje cikin nadi: Cewar Atiku Credit: @atiku
Source: Twitter

DUBA NAN: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

Majalisar zartawa ta ƙasar nan ta amince da fidda kuɗaɗe kimanin $1.5 biliyan don gyara babbar ma'aikatar ta ce man fetur dake Patakwal, babban birnin jihar Rivers..

Minista Sylva yace, za'a yi aikin gyaran ne a mataki uku, watanni 18, watanni 24, da kuma watanni 44, ya kuma bayyana cewa kamfanin italiya aka baiwa aikin, wanda kwararru ne a fannin.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel