Ramadan: Gwamnan APC Ya Ware N2.8bn Domin Dafa Abincin Buda Baki, Ya Kafa Kwamiti
- Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya bayyana kudurinsa na ciyar da talakawa da marasa galihu a jihar na tsawon kwanakin watan Ramadan
- Gwamna Namadi ya amince da kashe Naira biliyan 2.8 domin gudanar da shirin buda bakin yayin da ya kafa cibiyoyin ciyar da abinci guda 609
- Legit Hausa ta tattauna da Bamai Dabuwa, daga mazabar Kirikasamma da ke jihar Jigawa domin jin ra'ayinsa kan wannan shirin ciyarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya ware Naira biliyan 2.83 domin girka abincin buda baki na musamman a wannan wata na Ramadan.
Gwamnan ya ce ya kudiri aniyar shirya abincin buda bakin ne domin ciyar da talakawa da marasa galihu a jihar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai na jihar jigawa, Sagir Musa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufar wannan shirin ciyarwan Ramadan
Kwamishinan ya bayyana cewa an dauki matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba.
A cewarsa, shirin ciyarwar a lokacin azumi zai rage radadin da tashin farashin abinci ya haifar wa al'ummar jihar.
Musa ya ce an kafa cibiyoyin ciyar da abinci guda 609, inda za a mayar da hankali wajen samar da abinci kala uku ga talakawa da marasa galihu 182,700 a kullum.
Ramadan: Mutane miliyan 3.8 za su amfana
Daily Post ta ruwaito kwamishinan na cewa za a samar da cibiyoyin ciyar da abinci na musamman a dukkanin manyan makarantun jihar 10.
Ya kuma bayyana cewa za a aiwatar da shirin ciyarwar ne na tsawon makwanni uku inda ake fatan mutane miliyan 3.8 ne za su ci gajiyar shirina
Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta kuma ware Naira biliyan 1.125 domin siyan karin shinkafa da taliya da za a ajiye na 'ko ta kwana' domin samar da isasshen abinci a fadin jihar.
An kafa cibiyoyi 2 a kowace gunduma
Tun da fari, Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnatin Jigawa ta ce za ta ciyar da mutane 171,900 a kullum a cikin watan Ramadan.
Gwamna Umar Namadi, ya bayyana haka a wajen bikin raba kayan tallafi ga mazauna garin Dutse da ke jihar Jigawa.
Ya ce gwamnati ta samar da cibiyoyi biyu a kowace gundumar zabe domin gudanar da shirin, inda ya ce kowace cibiya ana sa ran za ta ciyar da akalla mutane 300 a kullum.
Abun da 'yan Jigawa ke cewa
Bamai Dabuwa, daga mazabar Kirikasamma da ke jihar Jigawa ya ce wannan shirin ciyarwa zai zama hanyar samun abinci ga talaka da almajirai a jihar.
A cewarsa, mutane na cikin wani mawuyacin hali na rashin kudi da abinci, yayin da a hannu daya kayan abinci suka yi tsada a kasuwa.
"Wannan abu ne mai kyau, musamman idan ka lura da cewa mutane suna cikin mawuyacin hali, ciyar da su a wannan matan ba karamin taimaka wa zai yi ba.
"Akwai almajirai da marasa galihu, kuma na ji an ce za zabi masallatai biyu a kowacce maza ba don raba wa mutane 600 abinci, gaskiya an taimaka sosai."
Duk da cewa har yanzu ba a kai ga fara rabon abincin ba, a cewar Dabuwa, gwamnatin Jigawa ta yi abun da ya dace na taimakawa talaka a irin wannan lokaci.
Jigawa: An rage lokutan zuwa aiki
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya rage lokutan da ma'aikatan jihar za su rinka zuwa aiki da tashi a wannan wata na Ramadan.
Gwamnan ya yi nuni da cewa rage lokutan zuwa aikin zai ba ma'aikata damar gudanar da ibadar azumi cikin kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng