Rashin Tsaro: Gwamnonin Arewa 19 Sun Gana da Ribadu, Sun Fusata da Yadda Ake Yaki da Ta’addanci

Rashin Tsaro: Gwamnonin Arewa 19 Sun Gana da Ribadu, Sun Fusata da Yadda Ake Yaki da Ta’addanci

  • Yayin da matsalar tsaro ta addabi Arewa, gwamnonin yankin 19 sun gana da mai ba Shugaba Tinubu shawara a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu
  • Gwamnonin sun bukaci sauya fasalin yadda ake yaki da ta’addanci a yankin inda suka koka kan yadda matsalar ke kara kamari a yankin
  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya wanda shi ne shugaban gwamnonin yankin shi ya bayyana haka a yau Alhamis 14 ga watan Maris

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Mai ba Shugaba Tinubu sharawa a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu ya gana da gwamnonin Arewacin Najeriya 19, cewar Punch.

Yayin ganawar wanda ya ta’allaka kan yadda za a dakile matsalar tsaro, gwamnonin sun bukaci sauya fasali a kokarin dakile matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC zai rage farashin kayan abinci da 25% yayin da aka fara azumi

Gwamnonin Arewa 19 sun bukaci sauya fasalin yaki da ta'addanci a yankin
Gwamnonin Arewa 19 sun gana da Nuhu Ribadu kan tsaro a Najeriya. Hoto: Northern Goovernors Forum.
Asali: Facebook

Korafin gwamnonin Arewa kan matsalar tsaro

Shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya koka kan yadda rashin tsaron ke kara dagulewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Inuwa ya bayyana haka ne a yau Alhamis 14 ga watan Maris bayan ganawa da Nuhu Ribadu da hafsoshin tsaron Najeriya.

Gwamnonin sun bukaci a sauya fasalin yaki da rashin tsaron da ya addabi yankin musamman garkuwa da mutane, cewar PM News.

Gwamna Inuwa ya ce sun yi ganawar ce da Ribadu domin neman sake fasalin dakile rashin tsaron da ke damun yankin.

Makasudin ganawar gwamnonin Arewa v Ribadu

“Makasudin wannan ganawa tsakanin mai ba da shawara a bangaren tsaro da gwamnoni ita ce kawo wani tsari na dakile matsalar tsaro.”
“Wannan ya shafi rashin tsaro wanda ya na da girma sosai musamman sace-sace a yankin Arewa maso Yamma ya kamata a sauya tsarin dakile matsalar.”

Kara karanta wannan

Bayan saukar da kai da amsa gayyatar Majalisa, Wike ya fadi gaskiyar lamarin rashin tsaro

- Inuwa Yahaya

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Uba Sani na jihar Kaduna da Umara Zulum na jihar Borno sai Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Sauran sun hada da Dikko Radda na jihar Katsina da Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da sauransu, cewar Leadership.

Gumi ya bukaci sulhu da ‘yan bindiga

Kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana aniyarsa na jagorantar sulhu da ‘yan bindiga yayin da aka sace dalibai 285 a jihar Kaduna.

Gumi ya gargadi Shugaba Tinubu da kada ya yi kuskure irin na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na kin amincewa da sulhun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.