Tattalin Arziki: Darajar Naira Na Ƙara Zurarewa Ƙasa Yayin da $1 Ta Haura Zuwa N1,620
- Darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi ta gwamnati da ta bayan fage na ci gaba da sunkuya wa ƙasa yayin da dala ke tashi sama
- Tsakanin Talata da Laraba kawai, Naira ta fadi da N12.56, bayan an yi hada-hadarta a kan N1,603.38/$1 zuwa N1,615.94/$1
- Masu shigo da kaya zuwa Najeriya na shan wahala wajen mallakar dalolin da suke bukata, wanda ya sa ake fargabar kudin kaya na iya karuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Darajar Naira ta sunkuya ƙasa zuwa N1,620 a kan kowacce $1 a kasuwar canji, sabanin yadda aka canja $1 kan N1,615 a ranar Talata.
Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa darajar kudin ƙasar ya sauka zuwa N1,615.94 a kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NAFEM).
Yadda aka yi cinikin Dala a makon nan
Wani rahoto da FMDQ ya fitar ya nuna cewa darajar Naira ta fadi daga N1,603.38/$1 zuwa N1,615.94/$1 a ranar Talata, kenan an samu faduwar N12.56.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darajar Naira sai da ta fadi warwas zuwa N1,635/$1 a kasuwar, amma daga bisani ta ƙara daraja zuwa N1,500/$1, inda aka samu bambancin N135.
Haka kuma, yawan dalar Amurka da aka yi hada-hadarta a ranar Talata ya haura da kaso 103.5% daga $122.18m zuwa $248.75, kenan an samu yawan cinikayya a ranar.
Akwai karancin dala a hannun 'yan kasuwa
Rahoton The Nation ya nuna cewa Naira na ci gaba da faduwa a kasuwannin hada-hada na gwamnati da na bayen fage sakamakon karancin dala a kasuwannin.
Masu shigo da kaya Najeriya na shan wahala wajen samun kuɗin da ake buƙata daga kasuwar FX ta gwamnati da ma kasuwar bayen fage.
Wannan kuwa a mahangar masu sharhi kan tattali arziki, zai iya haifar da tsadar kayayyaki a kasar musamman wadanda ake shigowa da su daga waje.
Fabrairu/Maris: Dala ta tsaya waje daya
Idan muka yi la'akari da wani rahoto na Legit wanda ya nuna cewa an yi cinikin Naira kan 1,600/$1 ranar 15 ga watan Fabrairu, za mu iya cewa canjin dala zuwa Naira ya tsaya a waje daya ne.
A wancan watan, ana musayar Naira da dala akan farashin da ya kai N1,533/$1 zuwa N1,590/$1 a ranar Laraba a kasuwar bayan fage, inda har ta kai N1600/$1 a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng