Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Na Bada Tallafin N500,000 Ga Matasa? Gaskiya Ta Bayyana

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Na Bada Tallafin N500,000 Ga Matasa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani shafi a manhajar Facebook ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya za ta bada tallafin N500,000 ga matasa
  • Batun bayar da tallafin na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da ji a jika kan cire tallafin man fetur da faɗuwar darajar naira
  • Sai dai, binciken da aka gudanar kan rubutun da aka yi a shafin, ya nuna cewa batun babu ƙanshin gaskiya a cikinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani shafin Facebook mai suna Solid Travels, ya wallafa wani rubutu kwanan nan inda ya ce akwai tallafin N500,000 da gwamnatin tarayya za ta ba matasan Najeriya.

Wannan iƙirari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kuka kan matsin tattalin arziƙi, wanda ya kai ga gudanar da zanga-zanga a faɗin jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Batun ba dalibai rance ya bi ruwa: Gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin aron kudin karatu

Gwamnatin Tinubu ba ta bada tallafin N500,000
Ba gaskiya ba ne batun bada tallafin N500,000 na gwamnatin Tinubu Hoto: Sean Gallup, Bloomberg
Asali: Getty Images

Bayan hawansa kan karagar mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur, wanda ya jawo ƙaruwar farashin man fetur da tsadar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darajar Naira ta kuma faɗi ƙasa warwas inda ta yi raga-raga a kan dalar Amurka.

Sama da shafukan mutum 3,700 ne suka mayar da martani kan rubutun na tallafin N500,000, yayin da ya samu sharhi fiye da 2,600 sannan an yada shi har sau 67 tun bayan yinsa a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2024.

Menene gaskiya kan bada tallafin N500,000?

Wani dandali na yin binciken gaskiya, Dubawa, ya gudanar da bincike kan lamarin bada tallafin.

Dandalin ya ce lokacin da ya shiga adireshin yanar gizon da aka sanya, bai samu wani abu a ciki da ya nuna a yi rajista ko duba cancantar samun tallafin na gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta yi martani kan barazanar kisan da wani malamin addini ya yi mata

Maimakon haka, sai shafin yanar gizon na -Petsmartgo.com- ya nuna yadda ƴan Najeriya za su iya samun biza a Amurka.

Ya ƙara da cewa masu yin kutse da masu zamba suna amfani da shafin yanar gizon don aikata munanan ayyuka.

Don haka, sai Dubawa ya gargaɗi masu amfani da yanar gizo da su da su yi hattara da shafin yanar gizon na bogi.

Gaskiya kan batun watsi da Naira

A baya rahoto ya zo kan binciken da aka gudanar bisa wani bidiyo mai cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce za a daina amfani da naira a koma amfani da dala a ƙasar nan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa bidiyon ƙirƙirarshi aka yi kuma shugaban ƙasan bai faɗi abin da aka yi iƙirarin ya ce ba a cikin bidiyon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng