Tsadar Rayuwa: Jerin Jihohi 12 da Suka Kara Kudi a Albashin Ma'aikatansu
- Bayan janye tallafin man fetur wanda ya haifar da tsadar rayuwa a Najeriya, akwai gwamnonin jihohi 11 da suka yi karin albashi
- Karin albashin dai an yi shi ne domin rage radadin wahalhalun da ma'aikatan gwamnati da iyalansu ke fuskanta a wannnan lokaci
- Yayin da jihohin Legas da Ondo ke biyan mafi girman karin albashi na N35,000, jihar Katsina, Adamawa da Ebonyi na biyan N10,000
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Akalla jihohi 12 ne ke biyan karin albashi ga ma’aikatansu a yayin da ake fama da tsadar rayuwa kamar yadda binciken jaridar The Nation ya nuna.
Jihohin Legas, Ekiti, Oyo, Osun, Ogun, Ondo, Enugu, Ebonyi, Adamawa, Jigawa, Gombe da Katsina na daga cikin jihohi 11 da aka tabbatar ma'aikata na samun karin albashi.
Tinubu ya nemi a yi karin albashi
A jiya Laraba ne jihar Neja ta amince da biyan karin albashin N20,000 ga kowanne ma’aikaci a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan janye tallafin man fetur da ya haifar da tsadar rayuwa, gwamnatin tarayya ta fara biyan karin albashin N35,000 ga ma’aikatanta.
A ranar Litinin Shugaba Bola Tinubu ya bukaci gwamnoni da su yi karin albashi ga ma’aikata gabanin kammala aikin da kwamitin sabon mafi karancin albashi.
Neja, Ogun sun yi karin albashi
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya yi wannan roko ne a lokacin da yake kaddamar da shirin noma da gwamna Umaru Bago ya kaddamar a garin Minna na jihar Neja.
A jiya ne Bago ya bayyana cewa ma’aikata a jihar sa daga wannan wata za su samu N20,000 a matsayin karin albashi.
Takwaransa na Ogun, Dapo Abiodun, tuni gwamnatinsa ta fara biyan N10,000 duk wata ga ma’aikatan gwamnati a matsayin karin albashi.
Sauran jihohin da suka yi karin albashi
Jihohin Legas da Ondo ne ke biyan mafi girman karin albashi na N35,000 ga ma’aikatansu yayin da Oyo da Enugu ke binsu a baya da N25,000.
Ekiti da Osun suna biyan N15,000 yayin da Jigawa, Gombe, Adamawa da Ebonyi ke biyan N10,000.
The Guardian ta ruwaito Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya amince da karin N10,000 ga ma’aikatan gwamnati da kuma N5,000 ga masu karbar fansho daga watan Janairu 2024.
Wasu daga cikin jihohin sun kuma kara wa ma’aikatan kananan hukumomi da ‘yan fansho albashin.
Gwamnati ta kara wa ma'aikata albashi
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aika karin albashi na wucin gadi da nufin rage masu radadin tsadar rayuwar da suke fuskanta a kasar.
A wani jawabin kai tsaye da shugaban kasar ya yi ga 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai, Bola Tinubu ya ce matsakaitan ma'aikata za su samun karin albashin N25,000.
Asali: Legit.ng