Borno: Gobara Ta Tashi a Sansanin ’Yan Gudun Hijira, an Yi Asarar Rayukan Kananan Yara

Borno: Gobara Ta Tashi a Sansanin ’Yan Gudun Hijira, an Yi Asarar Rayukan Kananan Yara

  • Gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke unguwar Muna a Maiduguri, jihar Borno a ranar Talata
  • Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta yi sanadin mutuwar yara biyu tare da haifar da firgici ga mazauna sansanin
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Borno da kuma gwamnatin jihar Borno sun ki yin wani tsokaci a hukumance dangane da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - A wani mummunan yanayi, gobara ta yi barna a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke unguwar Muna a Maiduguri, jihar Borno a ranar Talata.

Gobarar da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri, ta yi sanadin mutuwar yara biyu.

Kara karanta wannan

"Ana cikin tafiya": Yan sanda sun yi magana da wata ta tsunduma kogi a Legas

Sansanin 'yan gudun hijira na Borno
Gobara ta halaka kananan yara 2 a Borno. Hoto:Stefan Heunis/Contributor
Asali: Getty Images

'Yan sandan Borno ba su ce uffan ba

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wutar ta mamaye sansanin farat daya, lamarin da ya tada hankalin wadanda ke rayuwa a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu hukumomi ba su tantance musabbabin tashin gobarar ba, lamarin da ya bar tarin tambayoyi da aka gaza samun amsoshin su.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa rundunar ‘yan sandan jihar Borno da kuma gwamnatin jihar Borno sun ki yin wani tsokaci a hukumance dangane da lamarin.

Hare-haren 'yan Boko Haram a Borno

Sansanin 'yan gudun hijira na Muna, kamar sauran sansanoni, ya kasance mafaka ga dubban 'yan gudin hijira da rikicin Boko Haram ya raba su da muhallansu.

Sama da shekaru goma kenan jihar Borno na fama da munanan hare-haren ‘yan ta’addan, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Gobara ta lalata gidajen 'yan gudun hijira

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke jihar Borno, wadda ta babbake gidaje 1,000.

Hukumar SEMA ta tabbatar da cewa an yi asarar rayuka biyu a wannan gobarar, yayin da hukumomi ke ci gaba da binciken sababin tashin gobarar.

“Mun samar da buhunan shinkafa 500, barguna da sauran abubuwan da ba na abinci ba domin rage musu radadin halin da suka shiga."

- A cewar Dakta Barkindo Muhammad, shugaban hukumar SEMA na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.