FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa

FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa

- Gwamnatin tarayya ta shiga cikin matsananciyar fargaba sakamakon cutar Lassa da ta kunno kai a wasu jihohin Najeriya

- Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya tabbatar da yadda cutar ta fara barna musamman a 'yan makonnin nan har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama

- A jihar Delta, an samu masu cutar guda 23, wasu 17 kuma sun rasa rayukansu, yayin da mutane 51 suka mutu a jihar Enugu sakamakon zazzabin cutar

Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta a kan yadda masu zazzabin cutar Lassa a wasu jihohin Najeriya suka yawaita.

Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya bayyana yadda hankalinsa ya tashi, a Abuja lokacin taron PTF a kan cutar da kuma COVID-19.

A cewarsa, an samu sababbin masu zazzabin Lassa a wasu jihohi, musamman a lokacin ranin nan, Vanguard ta wallafa.

A cewar ministan, an samu sababbin masu cutar COVID-19 da aka tabbatar, guda 180, sannan wasu mutane 2 sun mutu a cikin sa'o'i 2 da suka gabata.

Kamar yadda yace, yanzu haka an tabbatar da masu cutar guda 697,544 a Najeriya.

"An sallami mutane 60,737 daga asibiti, yayin da yanzu haka ana cigaba da kula da mutane 2617 wadanda ke dauke da cutar a asibitoci da gidaje.

"Sai dai mutane 1,162 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar," yace.

Kamar yadda ministan lafiya yace, akwai sauran cututtuka masu matukar hatsari, kamar zazzabin Lassa, wanda alamun cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, tari, amai, ciwon kirji da sauran su.

Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu an lissafa mutane masu dauke da cutar guda 1131 a jihohi 27. A cikin satin nan, yawan masu cutar sun karu, an samu karin mutane 11, maimakon 3 na satin da ya gabata.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa
FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: TSA: Gwamnatin Bauchi ta bankado N1.48bn a wasu asusun bankuna 586

A wani labari na daban, wani ma'aikacin banki, mai suna Rowland Ogunebo, ya maka matarsa, Blessing, a wata kotun Ile-Tuntun da ke Ibadan ranar Alhamis saboda shigar banza da kuma bin maza, The Nation ta wallafa.

Ogunebo, mazaunin Kasumu Estate da ke Ibadan, ya yi magana a kotun, inda yace: "Bazan iya cigaba da zama da blessing ba. Saboda ba ta mutunta 'yan uwana. Ba ta yin shiga irin ta matan aure. Tana saka guntayen buje da matsattsun riguna."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel