Hanyoyi 12 da mutum zai bi don kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa

Hanyoyi 12 da mutum zai bi don kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa

Kamar yadda muke ta samun labarai, annobar zazzabin Lassa wacce ake samu daga jikin bera na ci gaba da yaduwa a wasu sassan kasar nan. Harma an samu rahoton mace-macen mutane da dama.

Wannan ya sa muka lalubo hanyoyin da mutum zai bi domin kare kansa daga kamuwa da wannan cuta.

Ga su kamar haka:

1. A yi kokarin raba beraye da cikin gida: Kada a yi sakaci har beraye su samu wurin zama a cikin gida.

2. A dunga bari abinci yana dahuwa sosai: A rika cin abin da aka dafa ya dafu sosai.

3. A toshe duk wani rami a gida don hana beraye sumun mafaka

4. Taba mataccen bera ko mai rai da hannu na iya sa a kamu da cutar Zazabin Lassa.

Hanyoyi 12 da mutum zai bi don kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa
Hanyoyi 12 da mutum zai bi don kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa
Asali: UGC

5. A kula da yawan tsaftace gida da kewayen sa: Barin datti a gina na kawo beraye ko daga waje ko daga wani gida.

6. A dunga ajiye abinci a wuri mai murfi: Barin abinci a bude kan kai bera ya ci, kuma har yay i fitsari ko kashi a kai.

7. A guji cin kayan marmarin da bera ya gutsira: Hakan ganganci ne sosai, don haka a guji ci ko da kuwa an wanke.

8. A dunga wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsafta: Dama wannan na cikin matakan farko na tabbatar da tsafta a jikin mutum.

9. A dunga rufe kwandon zuba shara: Beraye na shawaginsu cikin kwandon shara, su na cin sauran abincin da aka zubar.

10. A guje kusantar wanda ya kamu da cutar: Likita ne kadai zai iya kusantar wanda ya kamu da zazzabin lassa. Don haka a kiyaye.

11. Garzayawa asibiti ya fi a tsaya ana kame-kamen shan magani a gida idan babu lafiya.

12. A guji shanya abinci a waje kuma a bude a kasa domin hakan illa ce, babba sannan shanya abinci a kasa kan haifar da cututtuka.

KU KARANTA KUMA: Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai: APC ta sake lamunce wa Doguwa

A halin da ake ciki, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar akalla mutane 41 ne suka rasa rayukansu a sassan Najeriya daga farkon shekarar 2020 kawo yanzu.

Ministan Ilimi, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai a sakatariyar ma'aikatar dake Abuja.

Yayinda yake bayani kan yaduwar zazzabin, ya bayyana cewa akwai likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya cikin matattun 41 kuma akalla mutane 258 sun kamu da cutar a jihohin Najeriya 19.

Ya yi kira ga yan Najeriya gaba daya su kasance masu tsafta da kare kayan masarufinsu daga kashi da fitsarin beraye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel