'Yan Bindiga Sun Nemi Naira Tiriliyan 40 da Abu 2 a Matsayin Kuɗin Fansar Mutum 16 a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Nemi Naira Tiriliyan 40 da Abu 2 a Matsayin Kuɗin Fansar Mutum 16 a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun nemi a haɗa masu Naira tiriliyan 40 a matsayin kuɗin fansar mutum 16 da suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna
  • Maharan sun sace waɗannan mutanen ne daga kauyen Gonin Gora da ke ƙaramar hukumar Chikun ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024
  • John Yusuf, wani shugaban al'umma a kauyen Gonin Gora, ya ce sau biyu ƴan bindiga suka kai masu hari a mako ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Miyagun ƴan bindigan da suka yi garkuwa da mutum 16 mazauna garin Gonin Gora a jihar Kaduna, sun nemi kuɗin fansa mai ɗaga hankali.

Kamar yadda Vanguard ta tattaro, ƴan bindigan sun nemi fansar Naira tiriliyan 40, motocin Hilux guda 11 da babura 50 kafin sako mutum 16 da ke hannun su.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar alƙur'ani sun turo saƙo mara daɗi

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Kuɗin fansar da ƴan bindiga suka nema a Kaduna ya zarce hankali Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

A ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Gonin-Gora, wani yanki da ke cikin garin Kaduna a karamar hukumar Chikun, suka sace mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bukatar kudin fansa na zuwa ne kwanaki hudu kacal bayan an yi garkuwa da wasu ɗalibai 287 a Kuriga, wani ƙauye a yankin Chikun.

Abubuwan da suka nema a matsayin fansa

Wani shugaban al’ummar yankin, John Yusuf, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake hira da jaridar The Nation ta wayar tarho a ranar Litinin a Kaduna.

"Yan bindigan sun tuntubemu. Suna neman Naira tiriliyan 40, motocin Hilux 11, da babura 150 kafin su sako mutane 16 da suke tsare da su.
"Ina za mu samu wannan maƙudan kuɗin? Ko da garin mu muka sayar gaba daya, ba za mu iya tara Naira tiriliyan 40 ba. Hatta Najeriya a matsayin ƙasa ba ta taba yin kasafin Naira tiriliyan 40 ba."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama hatsabiban masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a Arewa

- John Yusuf.

Yadda maharan suka shiga Gonin Gora sau 2

A cewar shugaban al'umma a yankin, maharan sun kai farmaki ƙauyen Gonin Gora sau biyu a cikin mako ɗaya.

A rahoton Daily Trust, Yusuf ya ci gaba da cewa:

"Sun sace mutane sau biyu a tsakanin kwanaki hudu, a harin farko sun tafi da mutum uku yayin da karo na biyu suka ɗauki wasu mutum 13, jimulla mutane 16 kenan."

Yusuf ya bayyana damuwarsa kan yawan jejin da suka haɗa kauyen da kuma ƙaramar hukumar Birnin Gwari, ya buƙaci a kafa sansanin sojoji.

Dubun masu garkuwa 2 ta cika a Adamawa

A wani rahoton kuma Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane biyu da ake nema ruwa a-jallo kan aikata miyagun laifuffuka a jihar Adamawa

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce jami'ai da haɗin guiwar mafarauta sun kama su ne bayan tattara bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262