Fada Ya Kaure Tsakanin Garuruwan Neja Saboda Mace, An Yi Kone-Kone Har da Kashe Mutum 2

Fada Ya Kaure Tsakanin Garuruwan Neja Saboda Mace, An Yi Kone-Kone Har da Kashe Mutum 2

  • An samu hatsaniya tsakanin mutanen kauyen Tswako Makun da na Gbangba Dzuko, a karamar hukumar Gbako ta jihar Neja
  • Rikicin ya samo asali ne bayan wani matashi 'dan Gbangba Dzuko ya yi kokarin sumbatar wata amarya ana tsaka da biki a kauyen Tswako Makun
  • Lamarin ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane biyu sannan an yi asarar dukiyoyi masu yawan gaske

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Rahotanni sun kawo cewa fada ya kaure tsakanin al'ummar kauyen Tswako Makun da na Gbangba Dzuko, duk a karamar hukumar Gbako a jihar Neja.

A yayin karon ne aka kashe wani mutum mai suna Haruna Mohammed mai shekaru 40 daga kauyen Tswako Makun da Mohammed Kolo mai shekaru 20 a kauyen Gbangba Dzuko, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Emefiele ya cire daloli daga asusu babu amincewar Buhari ba, fadar shugaban kasa

An yi karo tsakanin garuruwa biyu a Neja
Fadan ya kaure ne a kan mace Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Me ya haddasa rikicin?

Rikicin dai ya fara ne a wajen shagalin bikin wani aure a Tswako Makun, lokacin da wani yaro 'dan kauyen Gbangba Dzuko ya yi yunkurin sumbatar daya daga cikin amaren da ake bikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaren suna tsaka da rawa da angwanensu ne lokacin da matashin ya nufi daya daga cikinsu da lalata, inda nan take abokan angon suka far masa da duka.

Majiyoyi sun ce an kwashi yaron zuwa babban asibitin Lemu, inda daga nan kuma aka tura su FMC Bida, amma sai ya ce ga garinku.

Mutuwar yaron ya fusata matasan kauyen Gbanga Dzuko, inda suka taru suka kai harin ramuwar gayya a kauyen Tswako Makun, lamarin da ya kai ga kisan mutum daya.

An yi asarar dukiya a karon

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kona babura 12, buhunan gyada, kayan abinci iri-iri, miliyoyin Naira da aka ajiye a gidaje da kuma wasu abubuwa masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

N585m: Jama'a sun taso EFCC da Tinubu a gaba saboda an ji tsit a binciken Edu

Haka kuma, wasu da dama sun jikkata ciki har da daya daga cikin angwanen, inda aka kwashe su zuwa babban asibitin garin Lemu.

Shugaban karamar hukumar Gbako ya yi martani

Kakakin shugaban karamar hukumar Gbako, Yahaya Alhaji Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ibrahim ya ce shugaban karamar hukumar Gbako, Hassan Muhammad ya ziyarci garuruwan biyu domin yi masu jaje da ta'aziyya.

Ya ce shugaban karamar hukumar ya kai ziyarar ne domin magance rikicin tare da dawo da zaman lafiya a garuruwan da abin ya shafa.

Ya kuma ce shugaban yankin ya roki mazauna Tswako Makun, da suka bar gidajensu, da su koma cewa an umurci jami'an tsaro da su kula da lamarin.

Martanin 'yan sanda kan lamarin

Zuwa yanzu ba a samun jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun ba, bai amsa sakon da aka tura masa kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Wani ya kashe makwabcinsa saboda akuya

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum mai suna Kolawole Akinsanya kan zargin hada kai da wasu bata gari don yi wa makwabcinsa, Lukmon Ajibola, dukan mutuwa.

Lamarin ya afku ne a yankin Ilepa da ke karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng